Matawalle Ya Karyata Danganta Shi da Ake Yi da Matsalar Tsaron Zamfara, Ya Soki Dauda
- Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle, ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa game da matsalar tsaron jihar Zamfara
- Matawalle ya karyata rahoton da ya ce ba za a yi nasarar tsaron Zamfara ba tare da shigarsa ba, yana kiran hakan da karya
- Ya zargi gwamnatin Zamfara da kin aiki tare da gwamnati ta tarayya, yana cewa Gwamna Dauda Lawal na kauce wa hadin kai a tsarin tsaro
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle, ya nuna damuwa game da karuwar rashin tsaro a kasar.
Matawalle ya karyata wani rahoton kafafen sada zumunta da ya ce ya yi ikirarin cewa shirin tsaro na Zamfara ba zai yi nasara ba idan bai shiga ba.

Source: Twitter
Martanin Matawalle kan rashin tsaron Zamfara
A cikin sanarwar mai taimaka masa, Ahmed Dan-Wudil ya fitar, Matawalle ya ce labarin karya ne da aka kirkira domin bata masa suna da kuma shirin gwamnatin tarayya, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce bai taba yin hira kan wannan magana ba, yana cewa rashin dabarar gwamna Dauda Lawal da kin hada kai da shi ne yake suka.
Matawalle ya zargi gwamnan da ware shi da sauran manyan jiga-jigai a shirin tsaro, duk da matsayin sa na minista da tsohon gwamnan jihar.
Ya ce rashin gayyatar sa a taron tsaro tare da ministan tsaro, Mohammed Badaru, abin takaici ne kuma ya nuna siyasantar da al’amura.

Source: Original
Matawalle ya soki gwamnatin Zamfara
Ministan ya soki gwamnatin jihar saboda tura jami’an tsaro ba tare da isasshen tattaunawa da Abuja ba, abin da ya ce na kawo tsaiko a yaki da ‘yan bindiga.
Ya ce wasu ‘yan siyasa na daukar nauyin labaran karya domin ta da hankula a Zamfara, tare da kira ga kafafen yada labarai su tabbatar kafin wallafawa, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
Matawalle ya ce a matsayinsa na wanda ke cikin harkokin tsaro, ba zai taba tunanin hana ci gaban jihar ba, musamman ganin yadda matsalar ta tsananta.
Ya ce:
“A matsayina na wanda ya tsunduma sosai cikin harkar tsaron ƙasa, babu wani dalili da zai sa in yi wa wani gwamna zagon ƙasa, balle ma a jihata wacce rashin ingantaccen shugabanci ya jefa ta cikin matsalolin tsaro da suka zama batun ƙasa baki ɗaya.”
Ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki tukuru don dawo da zaman lafiya, mayar da ‘yan gudun hijira, da karfafa tsaro a yankunan da suka tabarbare.
Matawalle ya yi jimamin mutuwar jigon APC
Kun ji cewa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya ziyarci dangin marigayi Umar S. Fada a Gusau da yan bindiga suka hallaka.
Matawalle ya ziyarci iyalan ne inda ya mika ta’aziyya tare da bayar da tallafin miliyoyin kudi da kayayyaki.
Sanarwar APC ta bayyana cewa marigayi Fada mutum ne nagari mai gaskiya da taimako, kuma rasuwarsa babban rashi ne ga jihar da ƙasa baki daya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

