Tinubu Ya Yi Alhinin Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, Ya Fadi Alherin da Ya Yi Masa

Tinubu Ya Yi Alhinin Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, Ya Fadi Alherin da Ya Yi Masa

  • Ana ci gaba da jimami tare da alhinin rasuwar sanannen malamin addinin Musulunci na darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bi sahun manyan mutanen da suka mika sakon ta'aziyyarsu kan rasuwar babban malamin na Musulunci
  • Mai girma Tinubu ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga kasa baki daya ba ga iyalansa ko mabiyansa kadai ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Shugaba Tinubu bayyana alhini da jin ya yi babban rashin sakamakon samun labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Shugaba Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaban kasa Bola Tinubu kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Sheikh Zakzaky ya fadi abin da ya ji kan rasuwar Shehu Dahiru Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu

Fitaccen malamin addinin Musuluncin na Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025, yana da shekaru 101 a duniya.

Al’umma daga sassa daban-daban na duniya sun aika da sakonnin ta’aziyya da addu’a ta kafafen sada zumunta kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musuluncin.

Iyalansa sun sanar da cewa za a yi jana'izar marigayin ne a ranar Jumma'a, 28 ga watan Nuwamban 2025.

Shugaba Bola Tinubu ya yi ta'aziyya

A cikin sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yi juyayin rasuwar jagoran Tariqar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin tushe na nagarta wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi.

Shugaban kasan ya ce rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi babban gibi ne ba ga iyalinsa da dimbin almajiransa kaɗai ba, har ma ga kasa baki ɗaya.

Ya kuma tuno yadda marigayin ya ba shi goyon baya da addu’o’i a lokacin shirin babban zaben shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki: "Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi babban rashi ne ga Musulmai

“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne, kuma muryar sassauci da hikima. A matsayinsa na malamin addini kuma masani a fassarar Alkur’ani Mai Girma, ya kasance mai kira zuwa zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi.”

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya yi jimamin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya ga dukkan mabiyan Sheikh a fadin kasar nan da ma wajen kasashen duniya bisa wannan babban rashi da aka yi.

Ya kuma yi kira gare su da su tsare koyarwarsa, su ci gaba da raya zaman tare cikin lumana, su karfafa dangantaka da Allah, kuma su kasance masu taimakon jama’a kamar yadda ya koyar.

Kwankwaso ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma madugun tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

​Kwankwaso ya bayyana cewa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, ya bar jama'a a cikin matukar takaici, amma dole a mika wuya ga hukuncin Allah SWT

Hakazalika, Kwankwaso ya kara da cewa rasuwar malamin babban rashi ne saboda rawar gani da ya taka wajen koyarwa, gyaran halayya da wayar da kan al’umma a duk faɗin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng