Abin da Gwamnatin Tinubu Ta Ce kan Juyin Mulki a Guinea Bissau, Ta Yi Gargadi

Abin da Gwamnatin Tinubu Ta Ce kan Juyin Mulki a Guinea Bissau, Ta Yi Gargadi

  • Gwamnatin Najeriya ta yi martani game da abin da ya faru a Guinea-Bissau inda aka cafke shugaban kasar
  • Najeriya ta nemi a gaggauta dawo da tsarin mulki, a kare masu sa ido na ƙasashen waje, tare da yin gargadi
  • Sojojin Guinea-Bissau sun ayyana karɓar mulki, sun rufe iyakoki bayan dakatar da zaɓe, yayin da Umaru Embalo ya ce an kifar da gwamnatinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta nuna rashin amincewa da juyin mulkin soja a Guinea-Bissau, tana bayyana shi a matsayin babban barazana ga dimokuraɗiyya.

Gwamnatin ta ce hakan barazana ce ga kwanciyar hankali na yanki gaba ɗaya inda ta ba da shawara.

Gwamnatin Tinubu ta yi Allah-wadai da juyin mulki a Guinea-Bissau
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Hakan na cikin sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Waje ta wallafa a shafin X a yau Alhamis 27 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Majalisa ta tsoma baki da Jonathan ya makale a kasar da sojoji suka yi juyin mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takaicin gwamnatin Tinubu kan juyin mulkin G/Bissau

Gwamnatin ta ce ta ji labarin ne cikin takaici tana cewa juyin mulkin ya karya tsarin mulki da ci gaban siyasar ƙasar.

Sanarwar ta jaddada cewa juyin mulkin ya sabawa ka’idojin ECOWAS, waɗanda ke haramta karɓar mulki ta hanyar da ba ta dace da tsarin ba.

Najeriya ta nuna goyon baya ga al’ummar Guinea-Bissau, tana kira da a dawo da tsarin mulki nan da nan tare da kare lafiyar duk wanda aka tsare.

Ta kuma yi kira da a kare masu sa ido na ƙasashen waje da ke ƙasar, tana mai bukatar a tabbatar da cikakkiyar tsaro da ‘yancinsu wajen gudanar da aikinsu.

Gwamnatin ta bukaci duk ɓangarori su nuna haƙuri, su bi hanyar tattaunawa, su kuma mutunta zaben da jama’a suka yi cikin lumana da sanarwar hukunta sakamakon zaɓe.

Gwamnatin Tinubu ba ta ji dadin juyin mulki a Guinea-Bissau ba
Embalo da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya, Hoto: Sulaimane Sissoco Embalo, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Guinea-Bissau: Gargadin da Najeriya ta yi

Najeriya ta gargadi masu juyin mulkin cewa za a hukunta su, domin aikinsu zai iya jefa ƙasar cikin rikici da lalata ci gaban siyasar da aka samu.

Kara karanta wannan

Jonathan ya makale a Guinea Bissau, sojoji sun rufe kasar bayan juyin mulki

Ta kuma tabbatar da cewa za ta yi aiki tare da ECOWAS da Tarayyar Afrika domin dawo da zaman lafiya da tsari cikin gaggawa a Guinea-Bissau.

A gefe guda, masu sa ido daga AU da ECOWAS sun la’anci juyin mulkin, suna cewa an yi niyyar dakile tsarin dimokuraɗiyyar da ake kokarin gina wa.

A ranar Laraba 26 ga watan Nuwambar 2025 sojojin ƙasar suka ce sun karɓi cikakken iko, suka rufe iyakoki, suka dakatar da zaɓe, tare da harbe-harbe kusa da fadar shugaban ƙasa.

Janar Denis N’Canha ya bayyana cewa rundunar haɗin gwiwa ta soji ta karɓi mulki, yayin da Embalo ya shaida ta waya cewa an kifar da gwamnatinsa.

Jonathan ya makale a Guinea-Bissau

Kun ji cewa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya makale a Guinea Bissau bayan sojoji sun sanar da juyin mulki.

Sojojin sun dakatar da tsarin zaɓe, yayin da daruruwan masu sa ido daga ƙasashen waje suka makale a filin jirgin sama.

An tabbatar da cewa Jonathan na cikin aminci, amma yana cikin rukuni na jami’an sa ido da ba za su iya barin ƙasar ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.