Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Girgiza Sanata Barau, Ya Fadi Yadda Ya Ji
- Sanata Barau Jibrin ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin babban rashi ga Musulunci da al’umma gaba ɗaya
- Mataimakin shugaban majalisar ya ce marigayin ya yi rayuwa mai cike da hidima, wa’azi, da ƙarfafa ilimin Alƙur’ani da tarbiyyar jama'a
- Hakan na zuwa ne bayan an bayyana cewa za a yi jana’izar marigayi Dahiru Usman Bauchi gobe a gidansa bayan sallar Juma'a
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi alhini kan rasuwar malamin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Sakon ta’aziyyar ya fito ne a sakamakon rasuwar babban malamin da ya yi fice a harkar wa’azi da koyar da Alƙur’ani a Najeriya.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Barau ya ce rasuwar Sheikh Dahiru ta zo a lokacin da al’ummar Musulmi ke bukatar jagorori masu hangen nesa kamar shi.
Barau ya fadi gudumawar Dahiru Bauchi
Sanata Barau Jibrin ya bayyana Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin malami mai zurfin ilimi da jajircewa wajen yaɗa koyarwar Alƙur’ani da wa’azi ba tare da gajiyawa ba.
Ya ce marigayin ya yi tasiri sosai a darikar Tijjaniyya, musamman wajen jagorantar miliyoyin mabiyansa cikin kwanciyar hankali da koyarwa bisa tsari.
A cewarsa, sadaukarwar marigayin wajen kafa makarantu, shirya tarukan wa’azi da kuma tallafin jinƙai ya taimaka wajen inganta rayuwar jama’a da kuma kula da matasa masu neman ilimi.
Ya ce irin wannan hidima da marigayin ya yi ta zamo ginshiƙi ga musulmai da dama, kuma za ta ci gaba da zama haske ga al’umma.

Source: Facebook
Sanata Barau ya kara da cewa Sheikh Dahiru ya zarce matsayin malami kaɗai, domin ya kasance uba, jagora, malami kuma abin dogaro ga miliyoyin mutane da suka amfana da rayuwarsa.
Sakon Barau ga iyalan Dahiru Bauchi
A sakonsa, Sanata Barau ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, almajiransa, al’ummar Musulmi da kuma duk wadanda suka samu shiriya ta hanyar rayuwar Shehu Dahiru Bauchi.
Mataimakin shugaban majalisa ya ce kalaman ta’aziyya ba za su iya cike gibin da marigayin ya bari ba, amma addu’a ce mafi muhimmanci a irin wannan lokaci.
Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin kurakuransa, ya ba shi matsayi mafi girma a Aljannar Firdausi, tare da ba iyalai da mabiyansa haƙurin jure wannan babban rashi.
Dikko Radda ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta yi ta'aziyya game da rasuwar Shehu Dahiru Usman Bauchi.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana rasuwar Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga Najeriya.
Ya mika sakon ta'aziyya ga gwamnan jihar Bauchi, iyalan marigayin da dukkan almajiran malamin a fadin duniya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

