Shawarar da Gwamna Nasir Ya Ba Daliban da 'Yan Bindiga Suka Saki a Kebbi

Shawarar da Gwamna Nasir Ya Ba Daliban da 'Yan Bindiga Suka Saki a Kebbi

  • Mai girma Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya mika daliban da 'yan bindiga suka sace a garin Maga zuwa ga hannun iyayensu
  • Nasir Idris ya bukaci 'yan matan da su dauki lamarin da ya faru da su a matsayin kalubale na rayuwa wanda bai kamata ya sare musu guiwa ba
  • Hakazalika, an bada tabbacin cewa babu daya daga cikinsu da aka ci zarafinta a yayin zaman da suka yi a hannun 'yan bindiga

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya bada shawara ga ’yan mata 24 da aka ceto na makarantar sakandaren mata ta GGCSS Maga, a karamar hukumar Danko/Wasagu.

Gwamna Nasir Idris ya bukaci daliban da aka ceto da kada su yi kasa a gwiwa wajen ci gaba da neman ilimi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kebbi ya yi magana kan batun biyan 'yan bindiga kudin fansa kafin sako dalibai

Gwamna Nasir Idris ya bukaci dalibai su ci gaba da karatu
Daliban da aka sace tare da Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi Hoto: Yahya Sarki
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce gwamnan ya yi wannan jan hankali ne yayin mika su ga iyayensu a fadar Gwamnati da ke Birnin Kebbi ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Gwamna Nasir ya gayawa daliban?

“Ina roƙonku ku ɗauki wannan lamari a matsayin ƙalubale na rayuwa. Kada ya rage muku kwazo wajen neman ilimi."
"Babu al’ummar da za ta ci gaba ba tare da ingantaccen ilimi ba. Haka ma dan Adam, ba zai bunƙasa ba tare da ilimi ba. Don haka wannan abin bai kamata ya rage muku kokari ba.”

- Gwamna Nasir Idris

Gwamna Nasir Idris ya kuma tabbatar wa iyayen yaran cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace don tallafa wa ’ya’yansu su ci gaba da karatu.

Ba a ci zarafin daliban ba

A nata jawabin, kwamishiniyar ilimin firamare da sakandare ta jihar, Dr. Halima Bande, ta bayyana cewa babu wata yarinya da aka ci zarafinta ko aka yi mata wani abu mara dadi yayin da suke hannun ’yan bindiga.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kebbi ta karbi ƴan matan sakandaren Maga 24 da aka kuɓutar

“Bayan an mika mana su daga hannun kwamandan Operation Fansan Yamma, mun garzaya da su asibiti domin cikakken binciken lafiya."
"Bayan gwaje-gwajen da likitoci suka yi, babu wadda aka samu da wata matsala ko cin zarafi. Dukkansu suna cikin koshin lafiya kuma an amince su koma hannun iyayensu.”

- Dr. Halima Bande

Gwamna Nasir Idris ya ba dalibai shawara
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu Hoto: @NasirIdrisKIG
Source: Facebook

Iyayen yaran sun yi godiya

Malam Iliyasu Garba Birnin Tudu, wanda yake da ’ya’ya huɗu a cikin wadanda aka ceto, ya gode wa Shugaba Bola Tinubu, Gwamna Nasir Idris, jami’an tsaro da kuma karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, bisa gaggawa da jajircewar da suka nuna wajen ceto ’yan matan.

“Mun yi magana da ’ya’yanmu, sun shaida mana cewa babu wanda ya taɓa su ko ya ci zarafinsu. Sun ce suna cikin koshin lafiya.”

- Mallam Iliyasu Garba Birnin Tudu

Malam Iliyasu wanda ke cikin farin ciki, ya gode wa gwamnatin jihar, mutanen Kebbi, malamai, da al’ummar Najeriya baki ɗaya bisa addu’o’i da kulawar da suka nuna a lokacin wannan kalubale.

Batun ceto dalibai a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi magana kan batun ba 'yan bindiga kudi kafin su saki daliban da suka sace.

Kara karanta wannan

Gwamna Nasir ya gano kuskuren sojoji kan rashin tsaro, ya ba su shawara

Gwamna Nasir ya bayyana cewa ko sisin kwabo gwamnati ba ta biya 'yan bindigan ba a matsayin kudin fansa.

Hakazalika, ya yi godiya shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kokarin da ya yi wajen ganin cewa an sako daliban.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng