Rashin Tsaro: ADC Ta Jefa Zafafan Tambayoyi ga Gwamnatin Tinubu

Rashin Tsaro: ADC Ta Jefa Zafafan Tambayoyi ga Gwamnatin Tinubu

  • Jam'iyyar ADC ta soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
  • Mai magana da yawun ADC na kasa ya bayyana cewa gwamnati na amfani da dabarun da ke karawa 'yan bindiga karfi
  • ​Mallam Bolaji Abdullahi ya yi zargin cewa gwamnati ba ta gayawa 'yan Najeriya gaskiya kan matsalar rashin tsaro

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta soki yadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke tafiyar da batun tsaro a kasar nan.

Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnati da amfani da dabarun da ke kara ba ‘yan bindiga damar bunkasa tattalin arzikinsu.

ADC ta soki gwamnatin Shugaba Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC, @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC ta taso Bola Tinubu a gaba

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi matsayin da 'yan bindiga suka samu a gwamnatin Tinubu

Bolaji Abdullahi ya ce manufar rufe makarantun gwamnati alama ce ta mika wuya ga akidar Boko Haram.

Ya ce ADC na taya iyalai da al’ummomin da aka kubutar da ‘yan uwansu farin ciki, musamman waɗanda aka sace a Kwara, da ɗaliban da aka yi garkuwa da su a Kebbi.

"Dole mu maimaita matsayarmu tun farko cewa waɗannan sace-sacen bai kamata su faru ba, da gwamnati ta cika nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata.”

- Mallam Bolaji Abdullahi

ADC ta ce halin da ake ciki yanzu sakamakon gwamnati ce da ta shagaltu da siyasa, tana aiki ba kamar gwamnati mai wakiltar jama’a ba, sai kamar wata kungiyar mamaya.

“Abin al’ajabi shi ne sai da maganar shugaban Amurka Donald Trump mai zafi, kafin gwamnati ta yi wani karamin martani.”

- Bolaji Abdullahi

ADC ta nuna shakku kan gwamnatin Tinubu

Game da sakin wadanda aka yi garkuwa da su, jam'iyyar ta ce akwai rikitarwa kan mabanbantan bayanai da suke fitowa daga jami'an gwamnati, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

Kara karanta wannan

'Maganganun Tinubu ne suka jawo': Ministan Buhari kan karuwar rashin tsaro

“Mabanbantan bayanai daga jami’an gwamnati daban-daban sun nuna cewa gwamnatin tarayya ba ta faɗa wa ‘yan Najeriya gaskiya game da yadda aka saki mutanen da aka sace.”

- Bolaji Abdullahi

An zargi gwamnatin Tinubu kan 'yan bindiga

ADC ta zargi gwamnati da tattaunawa da ‘yan ta’adda, tana mai cewa kalaman Sufeto Janar na 'yan sanda, cewa maharan coci a Kwara ba a kama su ba saboda ‘sun fito tattaunawar zaman lafiya da kansu’, abin tayar da hankali ne.

Haka kuma ta yi suka ga maganar mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, wanda aka ruwaito yana cewa an saki mutane ne saboda gwamnati da jami’an tsaro 'sun roke su cikin lalama'.

“Shin gwamnatin Najeriya na biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda? Mene ne abin da aka ba su kan mika makamansu?"
"Kuma idan ma sun mika bindigu, me zai hana su sake samo sababbi su ci gaba da laifi, muddin ba a kama su tare da hukunta su ba?”

- Bolaji Abdullahi

ADC ta ragargaji gwamnatin Bola Tinubu
Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

Wace matsala jam'iyyar ADC ta hango?

ADC ta yi gargadi cewa idan tattaunawa da ‘yan bindiga ita ce sabuwar dabara ta gwamnati wajen yaki da ta’addanci da yawaitar sace-sace, to lallai akwai matsala.

Kara karanta wannan

'Idan ba za ka iya ba ka sauka,' PDP ta taso Tinubu a gaba bayan rufe makarantu

“Najeriya na kan babbar hanyar kuskure mai haɗari. Wannan hanya ce ta gwamnati da ke neman maimakon fuskantar matsalar yadda ya kamata."
"Ta hanyar lallashi da yi wa ‘yan ta’adda rangwame, gwamnati na kara faɗaɗa tattalin arzikin ‘yan bindiga."

- Mallam Bolaji Abdullahi

Atiku ya soki Tinubu kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ragargaji Shugaba Bola Tinubu kan matsalar rashin tsaro.

Atiku ya bayyana cewa 'yan bindiga sun kafa gwamnati ta daban a karkashin mulkin Shugaba Tinubu.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma ce ceto daliban da aka sace a Kebbi ba abin murna ba ne, domin tun da farko bai kamata a ce an sace su ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng