Jira Ya Kare: Shugaba Tinubu Ya Nada Jakadu bayan Fiye da Shekara 2 a Mulki
- Bayan kusan fiye da shekara biyu a kan madafun ikon Najeriya, shugaban kasa Bola Ahmed ya aika da sunayen mutanen da zai nada jakadu ga majalisar dattawa
- Shugaba Tinubu ya aikawa majalisar dattawa da sunayen mutane uku da yake son ya nada jakadu domin tantancewa da tabbatarwa
- Nadin na zuwa ne bayan ofisoshin jakadancin Najeriya da ke kasashen waje sun kasance babu jakadu har na tsawon fiye da shekara biyu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Bola Tinubu ya aika da sunayen mutanen da yake so ya nada a matsayin jakadu ga majalisar dattawa.
Shugaba Tinubu ya aika da jerin sunayen mutane uku da ya zaɓa domin nada su jakadu, domin majalisar ta tabbatar da su.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Laraba

Kara karanta wannan
Tinubu ya nada shugaban NIA da ya shiga badakalar $43m lokacin Buhari a matsayin Jakada
Su waye Tinubu ya nada jakadu?
Sunayen da shugaban kasa ya aika sun haɗa da:
- Kayode Are – daga Jihar Ogun
- Aminu Dalhatu – daga Jihar Jigawa
- Ayodele Oke - daga jihar Oyo
Bayan karanta wasikar shugaban ƙasa, Akpabio ya ce:
“Jerin sunayen mutane uku ne zuwa yanzu, kuma ina da tabbacin sauran za su biyo baya.”
Shugaba Tinubu ya ce an yi waɗannan naɗe-naɗen ne bisa tanadin sashe na 171 (1), (2)(c) da (4) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa gyara).
Tinubu ya nemi amincewar majalisar dattawa
Ya roki majalisar dattawa da ta duba kuma ta tabbatar da waɗannan naɗe-naɗe cikin gaggawa, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar da labarin.
An mika wasikar zuwa ga kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawa, wanda aka umurce shi da ya dawo da rahoto cikin mako guda.
Wannan naɗaɗɗun sun zo ne sama da shekara biyu bayan Tinubu ya janye dukkan jakadu na Najeriya a watan Satumban 2023.

Source: Facebook
Ana sa ran za a tura sababbin jakadun zuwa muhimman ofisoshin jakadanci a sassan duniya bayan tabbatar da su, domin wakiltar Najeriya yadda ya kamata.
Tun bayan hawan Tinubu mulki a 2023, bai nada jakadu ba, lamarin da masu suka ke amfani da hakan wajen caccakar gwamnati.
Bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya Nigeria cikin jerin ƙasashen da ake kallon suna da tsanani kan ’yancin addini, da dama sun dora alhakin hakan kan rashin nada jakadu da gwamnatin Tinubu ta yi na tsawon lokaci.
Tinubu ya hana 'yan sanda gadin manya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya umarci janye jami'an 'yan sanda daga gadin manyan mutane (VIPs) a fadin kasar nan.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen karfafa samar da ‘yan sanda a yankunan karkara, inda rashin jami’an tsaro ya bar jama’a cikin hadari da hare-haren ‘yan bindiga.
Hakazalika, Shugaba Tinubu ya amince da daukar sababbin ‘yan sanda 30,000 a fadin kasa, tare da shirye-shiryen inganta cibiyoyin horarwa cikin hadin guiwa da gwamnatocin jihohi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

