Abinci Zai Wadata: Tinubu Ya Yunkuro a Najeriya, Ya Saki N50bn domin Samun Sauki

Abinci Zai Wadata: Tinubu Ya Yunkuro a Najeriya, Ya Saki N50bn domin Samun Sauki

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da ware makudan biliyoyin Naira domin kara inganta hanyoyin samar da abinci a Najeriya baki daya
  • Tinubu ya cire N50bn a shirin shugaban kasa na samar da abinci domin sauya tsarin habaka a iri Najeriya tare da karfafa samar abinci
  • Gwamnati ta bayyana shirin karfafa dakin gwaji, yaki da iri na jabu, da karfafa mata da matasa a kasuwancin iri a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa shirin shugaban kasa game da samar da iri domin karfafa samar da abinci.

Shugaba Tinubu zai ware N50bn a wani babban kudiri da zai sauya harkar iri a Najeriya tare da karfafa tsaron abinci.

Tinubu zai inganta hanyoyin samar da abinci a Najeriya
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana hakan a Abuja yayin bude taron 'Seed Connect Africa', wanda ya hada masana, gwamnati, manoma da masana kimiyya, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

'Ka tanadi hujjojI': Pantami zai iya shiga kotu da aka zarge shi da kisan dalibin ATBU

Yadda za a inganta iri ga manoma

A jawabin da aka karanto ta hannun Dr. Kingsley Uzoma, Shettima ya jaddada cewa tsarin samar da abinci ba zai yi nasara ba tare da ingantaccen tsarin iri ba.

Ya ce iri shi ne fasaha ta farko da ke tantance nasara ko faduwar noma, don haka dole a gina tsarin da ya dace da bukatun zamani.

Gwamnati ta kaddamar da shirin 'Seeds for Renewed Hope', wanda shi ne ginshikin sauya tsarin iri, tare da raba ingantattun iri ga manoma.

An bayyana burin gwamnati na kara yawan samar da iri na amfanin gona da 10% daga 2025 zuwa 2027 domin rage gibin bukata.

Tinubu ya fadi hanyoyin samar da wadataccen abinci a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Nasarar da ake samu bangaren iri, noma

Gwamnati na shirin karfafa dakunan gwaji, yaki da iri na jabu, da karin shiga matasa da mata a cikin harkar samar da iri, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ministan Aikin Gona, Abubakar Kyari ya ce shekaru 50 na bangaren iri na nuna jajircewar Najeriya wajen gina tsarin noma mai dorewa.

Kara karanta wannan

'Maganganun Tinubu ne suka jawo': Ministan Buhari kan karuwar rashin tsaro

Ya kara da cewa ingantaccen iri na da muhimmanci ga ajandar samar da abinci ta gwamnati, musamman ganin karin nasara a shirin NAGS-AP.

Kyari ya lissafo cigaban noman alkama, fara noman alkama da ruwan sama a Plateau, da kuma bunkasar Bankin Aikin Gona da sabbin kudade ga manoma.

Ya ce an riga ana ganin raguwar farashin kayayyakin abinci, alamar cewa ana tafiya daidai duk da cewa bukatar gyara zai ci gaba.

A 2023, Najeriya ta fitar da tan 4,000 na ingantattun iri zuwa kasashen waje, abin da ya samar sama da dala miliyan takwas wanda ke nuna an samu ci gaba.

Gwamnatin Tinubu ta ce farashin abinci ya sauka

Kun ji cewa Fadar shugaban kasa ta ce an samu ragin farashin kayan abinci da ya kai tsakanin kashi 45 zuwa 52 cikin 100 a faɗin ƙasar nan.

Ta ce manufofin tattalin arzikin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne suka taimaka wajen inganta samar da abinci da rage farashi.

Gwamnati na ganin saukar farashin a matsayin tabbaci na cigaban tattalin arziki da dorewar wadata ga ‘yan ƙasa baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.