Gwamnan Kebbi Ya Yi Magana kan Batun Biyan 'Yan Bindiga Kudin Fansa Kafin Sako Dalibai

Gwamnan Kebbi Ya Yi Magana kan Batun Biyan 'Yan Bindiga Kudin Fansa Kafin Sako Dalibai

  • An yi ta tambayoyi a kan ko gwamnati ta biyan 'yan bindiga kudin fansa kafin su sako daliban da suka sace a Kebbi
  • A sanarwar da gwamnati ta fitar, ta bayyana cewa an ceto daliban ne bayan kokarin da hukumomin tsaro suka yi
  • Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, wanda ya karbi daliban bayan an sako su, ya yi tsokaci kan batun biyan kudin fansa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya karɓi dalibai mata 25 na makarantar Maga da aka ceto daga hannun ’yan bindiga.

'Yan bindiga ne dai suka sace daliban bayan sun kai farmaki a makarantarsu da ke karamar hukumar Danku/Wasagu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kebbi ta karbi ƴan matan sakandaren Maga 24 da aka kuɓutar

'Yan bindiga sun sako daliban da aka sace a Kebbi
Gwamna Nasir Idris da daliban da aka sace a Kebbi Hoto: Bashir Ahmad, Yahya Sarki
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ambato Gwamna Nasir Idris, na tabbatar da sakin daliban daga hannun 'yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ceto daliban da aka sace a Kebbi

Tun da farko, fadar shugaban kasa ta sanar da sakin daliban cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, ya fitar a shafin X.

A cewarsa, Tinubu ya jinjinawa hukumomin tsaro bisa jajircewar da suka nuna wajen kubutar da dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su.

Ya ce Tinubu ya kuma umarci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen kubutar da sauran ɗaliban da ke hannun ’yan bindiga.

Shin gwamnati ta biya kudin fansa?

Gwamna Nasir wanda ya tabbatar da cewa ’yan matan suna cikin koshin lafiya, ya ce ba a biya ko sisin kwabo ba, sabanin yadda ake yadawa a kafofin yaɗa labarai.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, an ceto ɗalibai 25 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a Kebbi

Ya ce jami’an tsaro sun yi aiki ne bisa umarnin Shugaba Tinubu domin ceto ’yan matan cikin koshin lafiya.

“Ba a biya ko Kobo ba. Sojoji, DSS da sauran jami’an tsaro sun yi sintiri a daji suka ceto su ba tare da wani rauni ba.”

- Gwamna Nasir Idris

Gwamna Nasir ya yi godiya

Gwamna Idris ya nuna farin cikinsa tare da gode wa sojoji, DSS, NSCDC da ’yan sanda bisa rawar da su ka taka wajen ceton daliban, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da labarin.

Hakazalika ya kuma jinjinawa Shugaba Tinubu saboda jajircewarsa na ganin an dawo da ’yan matan cikin koshin lafiya da kuma kokarin tabbatar da tsaron kasa.

Gwamna Nasir Idris ya ce ba a biya 'yan bindiga kudin fansa ba
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu Hoto: @NasirIdrisKIG
Source: Facebook

Ya gode wa malamai da suka dage da addu’o’i domin nasarar aikin, tare da gode wa manyan mutanen da suka ziyarci jihar a lokacin tashin hankali, ciki har da shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, gwamnonin APC da Sufeto Janar na ’yan sanda.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Amurka ta yi magana kan sace dalibai a Kebbi da Neja

Gwamnan ya kuma yaba wa iyayen daliban kan haƙurinsu da amincewar da suka nuna cewa gwamnati za ta ceto ’ya’yansu lafiya.

Gwamna Nasir ya ba sojoji shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi korafi kan dabarar da sojoji ke amfani da ita wajen yaki da 'yan bindiga.

Gwamnan ya bukaci rundunar sojoji da ta canja dabarar da take amfani da ita wajen yaki da matsalar tsaro a jihar da ma Najeriya baki ɗaya.

Hakazalika, gwamnan ya yi kira da a binciki dalilin da ya sa aka janye dakarun sojoji kafin 'yan bindiga su kai hari a makarantar GGCSS Maga.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng