Atiku Ya Fadi Matsayin da 'Yan Bindiga Suka Samu a Gwamnatin Tinubu

Atiku Ya Fadi Matsayin da 'Yan Bindiga Suka Samu a Gwamnatin Tinubu

  • Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya koka kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
  • Atiku ya bayyana cewa sako daliban da 'yan bindiga suka yi ba abin murna ba ne face abin nuna damuwa kan halin rashin tsaro a kasa
  • Hakazalika, Atiku ya soki yadda hukumomin tsaro suka ki kashe 'yan bindiga duk da ikirarin cewa sun bi sawunsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Atiku Abubakar ya ce ’yan ta’adda da ’yan bindiga sun kafa wata gwamnati ta daban a zamanin Shugaba Bola Tinubu.

Atiku ya soki Tinubu kan rashin tsaro
Atiku Abubakar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @atiku, @DOlusegun
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Paul Ibe, ya fitar a shafinsa na X a ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

'Maganganun Tinubu ne suka jawo': Ministan Buhari kan karuwar rashin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya soki hadimin Tinubu

Atiku ya soki maganganun Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, waɗanda ya yi kan batun sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Onanuga ya ce gwamnatin tarayya ta zaɓi amfani da dabarar rashin amfani da karfi domin kare rayukan waɗanda ake garkuwa da su.

Atiku ya bayyana jawabansa a matsayin kokarin lulluɓe bala’in da ya faru a kasa tare da kawata gazawar gwamnati tamkar wata jarumtaka.

Tsohon ɗan takarar shugaban kasar ya ce yadda jami’an gwamnati ke ta murna da sakin daliban mata, ya nuna wata babbar matsala ta karawa kungiyoyin 'yan ta'adda karfin guiwa a sassan kasar nan.

“Gaskiya ita ce, sakin ’yan Najeriya da aka yi garkuwa da su ba abin murna ba ne; wani abin kunya ne da ke tuna mana cewa ’yan ta’adda yanzu suna yawo ba tare da tsoro ba."

Kara karanta wannan

"Sai an yi hakan": Malami ya gayawa Tinubu abin da zai kawo karshen matsalar rashin tsaro

"Suna tattaunawa a fili, suna sa sharudda, yayin da wannan gwamnati ke fitar da sanarwa domin ɓoye abin kunya.”

- Atiku Abubakar

Yadda Atiku ya kalubalanci Onanuga

Atiku ya kuma kalubalanci ikirarin Onanuga cewa jami’an tsaro sun bi sawun masu garkuwa da su a ainihin lokacin har ma sun yi magana da su.

“Idan DSS da sojoji suna iya bibiyar su a zahiri kuma sun yi magana da su, me ya hana kama su? Me ya hana tarwatsa su? Me ya hana kashe su a wurin?”

- Atiku Abubakar

Ya ce bayanan gwamnati suna nuna cewa lamarin garkuwa da mutane yanzu ya koma tamkar kiran waya tsakanin masu aikata laifi da jami’an gwamnati.

Atiku ya ce hakan na kara wa ’yan ta’adda karfin guiwa tare da rage wa jama’a amincewa da gwamnati.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi gargadin cewa wannan dabarar ta gwamnatin na iya zama barazana ga tsaron kasa.

Atiku ya yi kalamai masu kaushi kan gwamnatin Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar Hoto: Mustapha Sule Lamido
Source: Facebook

Wane matsayi 'yan bindiga suka samu?

“A zamanin Tinubu, ’yan ta’adda da ’yan bindiga sun zama gwamnati ta daban, suna tattaunawa, suna karɓar kudin fansa, suna barin wurin ba tare da an taɓa su ba, yayin da fadar shugaban kasa ke murnar biyayyarsu."

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi halin da ya shiga kan matsalar rashin tsaro a Arewa

- Atiku Abubakar

Atiku ya ce babu wata gwamnati mai kishin kasa da za ta yi shelar tattaunawa da ’yan ta’adda da take cewa tana bin diddigin su.

Ya ce barin masu garkuwa su koma cikin daji ba tare da an bibiye su ba zai tabbatar da sake maimaita irin wadannan hare-hare.

Atiku ya hana gwamnatin Tinubu sakat

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC.

Atiku ya zargi jam’iyya mai mulki ta APC da cewa ta bar kasar cikin mawuyacin hali fiye da duk wani lokaci tun tarihin siyasar zamani.

Hakazalka, Atiku ya ce ce zai yi duk mai yiwuwa wajen ceto Najeriya daga barnar da APC ta yi a kasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng