Yadda 'Yan Sanda Suka Saba Alkawarin Janye Jami'ai daga Gadin Manya Amma Ba a Cikawa

Yadda 'Yan Sanda Suka Saba Alkawarin Janye Jami'ai daga Gadin Manya Amma Ba a Cikawa

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci a janye ’yan sanda da ke gadin manyan mutane (VIPs) a fadin kasar nan.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin ne domin kara yawan jami’an da ke aiki a cikin al’umma, musamman yankunan da ke fama da karancin jami'ai.

An umarci 'yan sanda su daina gadin manyan mutane
Sufeto Janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun da jami'an rundunar Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook.

Wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na karfafa tsaron kasa da magance kalubalen tsaro da ake fuskanta yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai girma Bola Tinubu ya umarci a mayar da jami’an ‘yan sanda zuwa ainihin aikin su na kare al’umma a cikin yankunan da ake fama da karancin jami’ai.

Kara karanta wannan

Abu ya gagara: Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaron Najeriya

A cewar sanarwar, mataki zai taimaka wajen karfafa samar da ‘yan sanda a yankunan karkara, inda rashin jami’an tsaro ya bar jama’a cikin hadari da hare-haren ‘yan bindiga.

Hakazalika, a sabon tsarin duk wani babban mutum da ke bukatar tsaro daga gwamnati zai nemi jami’an tsaron hukumar NSCDC, maimakon ‘yan sanda sabanin yadda aka saba yi a baya.

Tarihin irin wannan umarnin a baya

An sha yin irin wannan sanarwa a zamanin gwamnatoci da dama a Najeriya, inda ake shirin maida jami’an ’yan sanda daga rakiyar masu madafun iko zuwa yankuna da ke da bukatar tsaro sosai.

Sau da dama, wadannan alkawura suna fitowa ne bayan korafe-korafen jama’a game da yadda ake amfani da ’yan sanda wajen gadin mutane 'yan kaɗan maimakon tsaron al'umma.

Kalubalen aiwatar da umarnin

Sai dai aiwatar da irin waɗannan manufofi na fuskantar matsaloli da dama ciki har da:

Adawa daga wajen manyan mutane

Manyan mutane da dama ba su yi amanna da kiran ofisoshin 'yan sanda ba don ba su kariya a lokacin da suka shiga cikin matsala.

Sun fi jin cewa samun jami'i a kusa da su ya fi samar musu da cikakken tsaro da natsuwa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda ruwan wuta da suka kutsa dajin da suka buya

Fargaba kan tsaron manyan mutane

Najeriya na fama da matsalolin garkuwa da mutane don karbar kudaden fansa, kuma 'yan siyasa da manyan mutane na daga cikin wadanda za a iya kai wa hari.

Hakan zai sanya su shiga fargaba kan tsaronsu idan har babu jami'an da ke gadinau

Bukatar samar musu da tsaro na daban

Hukumar 'yan sanda ba ta samar da wata runduna ta musamman ba wadda za ta zama makwafin jami'an 'yan sanda da ke gadin manyan mutane.

Samar da wannan runduna zai taimaka wajen ba manyan mutane kariya ba tare da kwashe jami'an 'yan sandan da ya kamata su ba jama'a tsaro ba.

Mece ce mafita?

Domin tabbatar da bin wannan umarnin na janye 'yan sanda daga gadin manya, akwai bukatar a yi abubuwa kamar haka:

Ayyana manyan mutane ta fuskar doka

Ya kamata majalisar tarayya ta yi doka wadda za ta bayyana su wanene manyan mutanen da suka cancanci samun kariyar 'yan sanda, kamar shugaban kasa, mataimakinsa, shugaban majalisar dattawa da sauransu.

Kara karanta wannan

Bayan ceto dalibai 25, shaidanin ɗan bindiga ya shiga hannun jami'an tsaro

Sauran da duk ba su a ciki, sai a cire su daga cikin wadanda 'yan sanda za su ba kariya.

Samar da rundunonin tsaro masu zaman kansu

Gwamnati ta taimaka wajen horar da rundunonin tsaro masu zaman kansu wadanda manyan mutane za su iya dauko hayarsu domin su ba su kariya.

Hakan na nufin har da ba su damar rike makamai masu kyau da samun hanyayoyin sadarwa masu inganci.

Shugabanni su zama abin misali

Ya kamata shugaban kasa, gwamnoni da shugabannin majalisa su bada misalai mai kyau ta hanyar rage jami'an da ke gadinsu.

Idan suka rage yawan masu gadinsu, hakan zai sanya dokar janye 'yan sanda daga gadin manyan mutane ta yi tasiri.

Yadda aka bada irin umarnin a baya

Shafin fij.ng ya zakulo lokutan da aka taba bada umarnin janye 'yan sanda daga gadin manyan mutane a baya.

Sai dai, wadannan alkawuran na janye 'yan sandan ba a cika su.

1. Sunday Arase (2015)

A ranar 20 ga Agusta 2015, watanni uku bayan hawa mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci a janye jami'an da ke gadin manyan mutane.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Tinubu ya ba sojoji umarnin mamaye dazuzzuka a Kwara da jihohi 2

A wajen wani taro da jam'ian ma'aikatar harkokin 'yan sanda da hukumar kula da ayyukan 'yan sanda, Buhari ya umarci IGP Sunday Arase da rage yawan jami'an da ke gadin manyan mutane.

Sai dai, daga baya hukumar kula da ayyukan ’yan sanda ta ce har yanzu ba ta aiwatar da umarnin gaba ɗaya ba, tana mai cewa ana tafiyar da shi a sannu a hankali.

2. Ibrahim K. Idris (2018)

A taron kwamishinonin ’yan sanda a Abuja a ranar 19 ga Maris 2018, IGP Ibrahim Idris ya sake bada umarnin janye jami'an da ke gadin manyan mutane.

“Saboda matsalolin tsaro da ake fama da su, dole mu sake duba yawan jami’an da ke gadin manyan mutane domin inganta aikin ’yan sanda a kasa."
"A bisa haka, ana bada umarnin janye dukkanin jami'an 'yan sanda da ke gadin manyan mutane, 'yan siyasa da jami'an gwamnati ba tare da bata lokaci ba."

- IGP Ibrahim Idris

3. Mohammed Adamu (2020)

IGP Mohammed Adamu ya bada umarnin janye jami'an 'yan sanda da ke gadin manyan mutane a shekarar 2020.

Ya bada wannan umarnin kwanaki biyu bayan zazzafar zanga-zangar #EndSARS.

Kara karanta wannan

Cikin rashin imani, Boko Haram sun guntule kan mata saboda zargin tsafi

4. Baba Usman Alkali (2021)

A watan Yuni 2021, IGP Alkali Usman ya umarci a janye ’yan sanda daga hannun fararen hula masu zaman kansu.

Usman Baba Alkali ya bukaci a janye 'yan sanda daga gadin manyan mutane
Tsohon Sufeto Janar na 'yan sanda, Usman Baba Alkali Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce tun da farko a watan Mayu 2021, ya bada umarnin janye jami'an 'yan sanda da ke gadin manyan mutane a jihohin Kudu maso Gabas da Rivers.

5. Kayode Egbetokun (2023)

A 2023 Shugaban ’yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun ya ba da umarnin janye dukkan ’yan sandan Police Mobile Force (PMF) daga gadin manyan mutane.

Kayode Egbetokun ya bayyana cewa za a samar da sabuwar runduna ta musamman domin gadin manyan mutane.

An fara janye jami'an 'yan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar tsaro ta musamman (SPU) ta bada umarni ga dukkanin jami'an 'yan sanda da ke gadin manyan mutane a Najeriya.

Rundunar ta umarce su da su gaggauta komawa sansani nan take ba tare da bata lokaci ba domin cika umarnin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Ba a gama da jihohin Kebbi da Neja ba, an sace mata a jihar Borno

Umarnin dai na zuwa ne bayan Mai girma Bola Tinubu ya umarci a janye dukkanin jami'an 'yan sandan da ke gadin manyan mutane.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng