Rigiji Gabji: Gwamnan Legas Ya Gabatar da Kasafin Kudin Naira Tiriliyan 4 na 2026

Rigiji Gabji: Gwamnan Legas Ya Gabatar da Kasafin Kudin Naira Tiriliyan 4 na 2026

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya gabatar da kasafin kuɗin jihar Legas na 2026 mai darajar Naira tiriliyan 4.2
  • An kiyasta samun kudin shigar jihar Legas ya kai sama da Naira tiriliyan 3.9, wanda ya haɗa da kaso daga tarayya
  • Legas ta ba da fifiko ga manyan ayyukan raya kasa, musamman a bangaren harkokin tattalin arziki da kiwon lafiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 ga majalisar dokoki.

Gwamnan ya bayyana kasafin a matsayin mai cike da hangen nesa da aniyar yada arziki ga mazauna jihar.

Gwamna Sanwo-Olu na mika kasafin 2026.
Sanwo-Olu yayin gabatar da kasafin kudin 2026. Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a X, gwamnan Legas ya ce kasafin ya zo ne domin tabbatar da ci gaba a shekara ta kusa da ƙarshe ta mulkinsa.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya gyarawa shugabannin Arewa zama kan rufe makarantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabin da ya gabatar wa ’yan majalisa, Sanwo-Olu ya bayyana cewa kasafin ya kunshi tsare-tsare da za su inganta rayuwa, bunkasa tattalin arziki da sauransu.

Legas ta yi kasafin Naira tiriliyan 4

Sanwo-Olu ya ce an kiyasta kudin shigan jihar a kan N3,993,774,552,141, wanda ya haɗa da N3.1tn daga kudin da za a samu a cikin gida da kuma N874bn daga gwamnatin tarayya.

Wannan adadi, a cewarsa, ya bar gibin kasafi na N243,332,457,167 da za a samar ta hanyoyin da gwamnati za ta tsara.

Ya ce an ware fiye da N2.18tn domin manyan ayyukan raya kasa, yayin da aka ware N2.05tn domin kudin gudanarwa, wanda ya shafi kudin ma’aikata, biyan bashi da sauran ayyukan gwamnati.

A bayaninsa, ya ce kudin wasu ayyukan gwamnati sun kai N1.084tn, kudin hakkokin ma’aikata sun kai N440bn, yayin da kudin biyan bashi suka kai kimanin N383bn.

An raba kasafin Legas zuwa bangarori

Gwamnan ya yi cikakken bayani kan bangarorin da za su amfana, inda ya ce an ware wa bangaren ayyukan gwamnati N847bn, yayin da tsaro da dokoki suka samu N147bn.

Kara karanta wannan

Shugaban Amurka, Trump ya kara daukar zafi, ya kira Najeriya da kalma mara dadin ji

Bangaren da ya fi kowanne samun kaso a kasafin shi ne harkokin tattalin arziki, wanda aka ware masa sama da N1.37tn domin ayyukan sufuri, masana’antu, kasuwanci da sauransu.

Gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu
Gwamna Sanwo-Olu yayin wani taro. Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Source: Getty Images

Sauran bangarori sun haɗa da muhalli N235bn, gidaje N123bn, kiwon lafiya N338bn, ilimi N249bn, wasanni da nishaɗi N54bn, da tallafawa marasa karfi N70bn.

Manufar kasafin Legas na 2026

Sanwo-Olu ya ce shekarar 2026 na da muhimmanci matuƙa domin ita ce shekarar kusa da ƙarshe kafin kare wa’adin mulkinsa, inda ya ce:

“Wannan lokaci ne da za mu tabbatar da nagarta da kammala manyan ayyukan da muka fara.”

Kano ta yi kasafin Naira tiriliyan 1

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnan jihar Kano ya mika kasafin kudin jihar ga majalisar dokoki.

Abba Kabir Yusuf ya mika kasafin kudin shekarar 2026 da ya haura Naira tiriliyan 1, karon farko a tarihin jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa yana fatan kawo ayyukan cigaba ga jihar Kano yayin mika kundin kasafin ga majalisa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng