Bayan Korar Ma'aikata, Ganduje Zai Kafa Hukumar Hisbah Mai Zaman Kanta a Kano

Bayan Korar Ma'aikata, Ganduje Zai Kafa Hukumar Hisbah Mai Zaman Kanta a Kano

  • Tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana shirin kafa sabuwar kungiyar tsaro domin inganta zaman lafiya a jihar
  • Ganduje da ke yi wa lakabi da Khadimul Islam zai kafa kungiya mai kama da Hisbah domin daukar ma’aikatan da gwamnatin yanzu ta kore su
  • An ce kungiyar za ta yi aikin wa’azi, taimakon gaggawa da inganta dabi’a, tare da karbar masu son shiga duk inda suka fito

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana shirin kafa wata kungiyar tsaro a jihar domin samar da zaman lafiya.

Majiyoyi sun ce Ganduje zai kafa kungiyar ce mai kama da hukumar Hisbah karkashin gidauniyarsa domin taimaka wa ma’aikatan da aka sallama.

Ganduje zai kafa hukuma mai kama da Hisbah a Kano
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Facebook

Musabbabin shirin kafa hukumar mai zaman kanta

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya gyarawa shugabannin Arewa zama kan rufe makarantu

Ganduje ya ce shirin na nufin daukar ma’aikatan Hisbah 12,000 da gwamnatin yanzu ta kora, yana mai jaddada cewa korar da aka yi musu babi adalci, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya bayyana haka ne lokacin karɓar rahoton alkaluman wadannan ma’aikata daga Dr Baffa Babba Dan-Agundi, shugaban kwamitin tantance wadanda abin ya shafa.

Dan-Agundi ya ce kwamitinsu ya tantance bayanai tare da tuntuɓar ma’aikatan da aka sallama, yana mai tabbatar da cewa duk sun kasance cikin wannan sabuwar tafiya.

Manyan 'yan siyasa da suka halarci taron

A martaninsa, Ganduje ya ce sabon tsarin zai kasance kamar Hisbah mai zaman kanta ba hukumar gwamnati ba, kuma za ta dauki sababbin mutane da ke sha’awa.

Taron ya samu halartar Nasiru Gawuna, Murtala Sule Garo da suka yi wa jam'iyyar APC takarar gwamnan Kano a zaben 2023.

An kuma ga shugaban APC Abdullahi Abbas, da Rabiu Sulaiman Bichi tare da wasu jiga-jigan jam’iyya da gwamnati.

Ganduje ya shirya ba ma'aikatan Hisbah da aka kora aiki
Tsohon shugaban APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Twitter

Wanda ake sa ran zai jagoranci hukumar

Ana sa ran tsohon kwamandan Hisbah, Ibn Sina zai jagoranci sabuwar kungiyar, wadda za a kira Khairun Nas, wacce za ta yi aiki ba tare da zama hukuma ba.

Kara karanta wannan

EU: Tarayyar Turai ta goyi bayan farfado da wasu kamfanonin Kano

Ibn Sina ya ce an kafa kwamitin tantance wadanda suka amince su shiga, kuma kungiyar za ta bude kofarta ga kowa ba wai korarru kadai ba.

Yadda za a rika ba sababbin ma'aikatan alawus

Game da alawus, ya ce aikin zai kasance na sa kai gaba daya, sai dai gudummuwa daga jama’a ko kungiyoyi na iya samar da tallafi ko kudaden na musamman.

Ya bayyana cewa ayyukan kungiyar sun haɗa da yada alheri, hana mummunan aiki, ba da agajin farko, wa’azi, da taimaka wa al’umma ta hanyoyi masu amfani.

Ganduje, APC sun goyi bayan Tinubu

Kun ki cewa Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci tarurruka da shugabannin APC na Kano inda suka amince da Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban kasa.

Ganduje ya umurci shugabannin kananan hukumomi da gundumomi su koma yankunansu domin bayyana goyon baya ga Bola Tinubu a bainar jama’a.

An samu manyan jiga-jigan jam’iyya a taron, sai dai wasu mutum biyu daga cikin fitattun ’yan siyasa ba su halarta ba, lamarin da ake ganin ya bar baya da kura.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.