Ana Wata ga Wata: 'Yan Bindiga Sun Shiga Jihar Kano, Sun Yi Garkuwa da Mata
- Mazauna wani kauyen Kano sun kwana cikin tashin hankali bayan ’yan bindiga sun kai masu farmaki tare da sace mutane
- 'Yan bindigar sun farmaki garuruwan da suka hada da Yan Chibi, Sarmawa da Gano, kuma sun sace mutanen da sun kai takwas
- Wani magidanci, Kabiru Usman ya ba da labarin yadda aka sace matarsa, 'yarsa, matar kaninsa da wasu mutanen gari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Rahotanni na nuni da cewa 'yan bindiga sun sace akalla mutane takwas a kauyen Biresawa da ke karamar hukumar Tsanyawa, jihar Kano.
Wata majiya mai tushe ta sanar da cewa 'yan bindigar sun kai hari kauyen Biresawa da misalin karfe 11:00 na daren Litinin zuwa 12:00 na safiyar Talata.

Source: Original
'Yan bindiga sun sace mutane 8 a Kano
Majiyar, wacce ta zanta da jaridar Daily Trust, ta bayyana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Sun kawo mana hari kamar yadda suka saba, kuma a bayanin da muka samu, sun saec maza biyu da mata shida. Har yanzu babu labarin inda suke."
Daya daga cikin 'yan uwan wadanda aka yi garkuwa da su, Kabiru Usman, ya ce maharan sun shiga kauyen ne ta makota, watau kauyen Tsundu.
"Sun kutsa cikin garin ne a kafa, dauke da miyagun bindigogi. Sun yi garkuwa da matata, Umma; yarinyata 'yar shekara 17, Fati; matar kanina da kuma wasu mata biyu.
"Mun yi iya kokarinmu na dakatar da su daga wannan harin amma makamanmu ba su taka kara sun karya ba, domin suna dauke da miyagun makamai.'
- Kabiru Usman.
Karashen rahoton na zuwa...
Ya kara da cewa mazauna garin sun sanar da 'yan sanda da sojoji cewa za a kawo masu hari bayan da suka samu bayanan sirri.
"Kafin a kai harin, mun samu rahoto cewa 'yan bindigar sun nufo kauyenmu, mun kuma sanar da jami'an 'yan sanda da sojoji, da ma sun ba mu lambobinsu mu rika kira idan wata matsalar ta taso."

Kara karanta wannan
"Akwai dalili": Hadimin Tinubu ya fadi abin da ya sa sojoji ba su iya farmakar 'yan bindiga
- Kabiru Usman.
'Yan bindiga sun kai hari kauyuka 3 na Kano
Wata majiya ta kuma shaidawa jaridar cewa kauyukan da 'yan bindigar suka farmaka a ranar sun hada da Sarmawa, Yan Chibi da kuma Gano, duk a karamar hukumar Tsanyawa.
Majiyar ta labarta cewa:
"Akalla 'yan bindiga 50 ne haye a kan babura suka farmaki garinmu na Yan Chibi suna harbi kan mai uwa da wani, lamarin da ya tilasta mutane tserewa don neman mafara.
"Daga bisani ne muka gano cewa sun sace mutanenmu, musamman mata, amma ba zan iya fadin adadin da aka yi garkuwa da su ba.
"Hakazalika, mun kuma ji cewa sun kai hari a wasu kauyukan inda nan ma suka yi garkuwa da mutane. Yanzu dai na nake magana, ba a samu asarar rai ba, amma tabbas sun sace akalla mutum 10."
Wata majiyar ta ce 'yan sa kai sun yi kokarin dakile harin amma abu ya gagara, sannan sun bi sahun 'yan bindigar, nan ma dai ba a samu nasarar cimma su ba.

Source: Facebook
Mutane sun daina brcci a garuruwan Kano
Akwai kuma wata majiya da ta shaidawa manema labarai cewa mutanen garuruwan yankin sun dade suna rayuwa cikin firgici tun bayan harin da haka kai Shanono da Bagwai da ke makotaka da su.
Majiyar ta bayyana cewa iyalai da dama sun hakura da bacci a garuruwansu, inda suke shiga cikin garuruwa su kwana, sai da safe su koma gida.
Wasu mazauna garuruwan sun nemi mafaka a garin Faruruwa ko kuma dai sun shiga cikin birnin Kano, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Kakakin rundunar 'yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa bai bai amsa kiraye-kirayen da aka yi masa ba har zuwa lokacin wallafa rahoton.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai hare-hare a wasu kananan hukumomi a Kano, lamarin da ya jawo kisan mutane uku da sace wasu.
Shugabannin yankin sun ce maharan na shigowa daga Katsina ta hanyoyin daji, suna kai farmaki duk da kasancewar dakarun tsaro a yankin.
Shugabannin yankin sun roki Shugaban Najeriya Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf su dauki matakin gaggawa kan lamarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


