Bayan Sace 'Yan Mata a Borno, 'Yan Ta'addan ISWAP Sun Kinkimo Batun Kudin Fansa
- 'Yan ta'addan kungiyar ISWAP da suka yi garkuwa da wasu 'yan mata a jihar Borno, sun tuntubi iyalansu don karbar kudin fansa
- Tsagerun 'yan ta'addan dai sun sako daya daga cikin 'yan matan ne domin samun hanyar da za su yi magana da 'yan uwansu
- 'Yan uwan 'yan matan da aka sace, sun bukaci gwamnati da jama'a su taimaka musu domin ba su da kudin da ake neman a biya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - 'Yan ta'addan ISWAP da suka yi garkuwa da ’yan mata 13 manoma a jihar Borno, sun bukaci a biya su kudin fansa.
'Yan ta'addan na ISWAP sun nemi kuɗin fansa na Naira miliyan 10, kamar yadda iyalan wadanda aka sace suka bayyana.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta ce dan uwan daya daga cikin 'yan matan da aka sace ne ya sanar mata da hakan a ranar Talata, 25 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan
"Akwai dalili": Hadimin Tinubu ya fadi abin da ya sa sojoji ba su iya farmakar 'yan bindiga
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maayakan ISWAP ne suka yi garkuwa ’yan matan a ranar Asabar, 22 ga watan Nuwamban 2025.
'Yan ISWAP sun nemi kudin fansa
Dan uwa ga ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ya ce sun samu bayanin ne daga wadda aka sako daga cikin 'yan matan.
“Ka san ba wai ta tsere da kanta ba ne. Su ne suka sake ta saboda sun gano cewa tana shayar da jariri.”
"Kafin ta bar wurin daya daga cikin ’yan ta’addan ya karɓe wayarta, ya ba ta sabon layi, ya umarce ta da ta saka shi a waya da zarar ta isa gida.”
"Ana saka layin a cikin waya, sai kira ya shigo daga masu garkuwa da mutanen suna neman Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansar sauran ’yan matan."
- Wata majiya
Ya ce wannan bukata ta jefa al’ummar yankin cikin tsananin damuwa.
"Mu talakawa ne manoma da muke neman abin da za mu ci. Ina za mu samo irin wannan kuɗi domin kuɓutar da waɗannan ’yan mata?”

Kara karanta wannan
Katsinawa sun sace iyalan ƴan ta'adda, an tilasta musayar mutanen da aka yi garkuwa da su
- Wata majiya

Source: Facebook
Ya roƙi gwamnati da masu hannu da shuni su taimaka wajen ganin an sako waɗannan matasan mata da ke cikin mawuyacin hali a hannun masu garkuwa da mutane.
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce bai samu bayanin lamarin ba tukuna, amma zai bincika ya dawo da bayanai.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar yankin cewa ’yan sanda suna yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da dawowar ’ya’yansu cikin koshin lafiya.
'Yan ta'adda sun yanka mata a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram na bangaren Ali Ngulde sun guntule kan wasu mata a jihar Borno.
'Yan ta'addan sun zargi matan da yin sihiri bayan sun same su da wasu layu a wuraren da ke karkashin ikon su a tsaunukan Mandara.
Wata majiya ta tabbatar da cewa matan sun fada hannun ‘yan ta’addan ne lokacin da suka gudanar da rangadin bincike a cikin al’ummar da suke iko da ita.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
