Buba Galadima Ya Gyarawa Shugabannin Arewa Zama kan Rufe Makarantu

Buba Galadima Ya Gyarawa Shugabannin Arewa Zama kan Rufe Makarantu

  • Jagoran NNPP, Buba Galadima, ya ce rufe makarantu saboda matsalolin tsaro rashin kishi ne da gazawar gwamnati
  • Ya zargi gwamnati mai-ci da mayar da hankali kan siyasa maimakon kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasa da suka zabe ta
  • Injiniya Buba ya nemi gwamnati ta inganta tsaro da fasaha maimakon yin watsi da makarantun yankin Arewacin kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A wani bayani da ya yi, jagoran jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi tir da matakin rufe makarantu a yankunan Arewa saboda yawaitar sace-sacen dalibai da hare-haren ’yan bindiga.

Ya bayyana wannan mataki a matsayin wani abin kunya da kuma rashin cika nauyin da gwamnati ta dauka na kare rayuwar ’yan kasa.

Jagoran NNPP, Buba Galadima
Buba Galadima yana wani jawabi a taron siyasa. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

Buba Galadima ya bayyana haka ne a wata hira da tashar Arise News ta yi da shi game da tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan

Satar dalibai a Kebbi da Neja, gwamnati ta rufe makarantun da ke iyaka da Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a halin da ake ciki, tabarbarewar tsaro a jihohi kamar Neja da wasu sassan Arewa ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta kasa bai wa batun tsaro muhimmanci.

Buba Galadima ya ce gwamnati ta gaza

A cewar Buba Galadima, gwamnatin tarayya ta gaza wajen kare al’umma, inda ya zargi shugabanni da mayar da hankali kan siyasa maimakon tsaro.

Ya ce:

“Gwamnati ta yi watsi da nauyin kare rayuka da dukiyoyi, ta kuma yi amfani da kashi 99 na lokacinta a harkokin siyasa.”

Ya bayyana rufe makarantu a matsayin “abin kunya ga gwamnati da hukumomi,” yana mai cewa abin da ya dace shi ne tsare su, ba rufe su ba.

Buba Galadima ya ce idan an ci gaba da yin haka, wannan na nuni da cewa gwamnati ta mika wuya ga miyagu.

Shawarin Buba Galadima ga gwamnati

Jagoran NNPP din ya yi suka kan tsarin gwamnati na dogaro da karfin soja kawai, ba tare da ingantacciyar hanyar samun bayanan sirri ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ra ki bin sahun jihohin da ke kulle makarantu, ta fadi matakin da ta dauka

Ya ce:

“Sun gwada nuna karfi, bai yi aiki ba. Lokaci ya yi da za su yi amfani da hankali da fasaha su kare ’yan kasa.”

Galadima ya kawo misali daga kasar China inda ya shaida yadda aka gano jaka da aka sace ta hanyar CCTV daga filayen jirage biyu cikin ’yan sa’o’i.

Hoton wata makaranta a jihar Gombe.
Makarantar Buhari Estate a jihar Gombe. Hoto: Legit
Source: Original

Punch ta wallafa cewa ya ce wannan misalin ya nuna yadda Najeriya ta kasa amfani da fasaha wajen inganta tsaro.

Maganar sace dalibai a Neja da Kebbi

Buba Galadima ya ce kafin sace dalibai a Neja akwai bayanan sirri kan motsin ’yan bindiga, amma jami’an tsaro suka kasa daukar mataki.

Ya kuma yi Allah wadai da yadda sojojin da aka tura makarantun suka bar wurin da aka ajiye su, yana mai cewa ya kamata a dauki mataki a kan irin wannan sakaci.

'Dan siyasar ya jaddada cewa tsarin tsaro na Najeriya ya tsufa, yana bukatar sauyi cikin gaggawa domin magance matsalolin kasar.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya fadi matsalar da ake fuskanta wajen kawar da rashin tsaro

Za a rufe makarantu a jihar Gombe

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe ta ce za ta rufe dukkan makarantu a ranar Juma'a mai zuwa.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da kai hare-hare makarantu a wasu jihohin Arewa ana sace dalibai da malamai.

Shugaban SUBEB na jihar ya bayyana cewa gwamna Inuwa Yahaya ya umarci a kammala jarrabawa kafin rufe makarantun.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng