Nnamdi Kanu: 'Yan Majalisa Sun Mika Bukatarsu ga Tinubu kan Jagoran Kungiyar IPOB

Nnamdi Kanu: 'Yan Majalisa Sun Mika Bukatarsu ga Tinubu kan Jagoran Kungiyar IPOB

  • Ana ci gaba da magana kan hukuncin da kotu ta yankewa jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu
  • Kungiyar 'yan majalisar wakilai na yankin Kudu maso Gabas sun shiga cikin sahun masu neman ayi masa afuwa
  • 'Yan majalisun sun gayawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, illar ci gaba da tsare Nnamdi Kanu a gidan gyaran hali

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar ’yan majalisar wakilai na Kudu maso Gabas sun mika kokon bsrarsu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan Nnamdi Kanu.

'Yan majalisun sun bukaci Tinubu da ya yi afuwa ga shugaban na IPOB, wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai kan laifuffukan ta’addanci da ake tuhumarsa da su.

'Yan majalisar wakilai na Kudu maso Gabas na son Tinubu ya saki Nnamdi Kanu
Jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta kawo rahoto cewa 'yan majalisar guda 42 sun bayyana hakan ne bayan wani zama da suka gudanar a ranar Litinin a majalisar dokoki ta kasa.

Kara karanta wannan

An yi yunkurin kashe alkalin da ya yanke wa Nnamdi Kanu hukunci? Kotu ta yi bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta yankewa Nnamdi Kanu hukunci

An yanke wa Kanu hukuncin ne makon da ya gabata bayan kotu ta same shi da laifi a kan tuhume-tuhumen ta’addanci guda biyar daga cikin bakwai da gwamnatin tarayya ta shigar a kansa.

Kafin yanke hukuncin, alkalin kotun, James Omotosho, ya umarci a fitar da Kanu daga zauren kotu saboda abin da ya kira halin ɗabi’a marar kyau a lokacin shari’ar.

'Yan majalisar Igbo na son a saki Kanu

'Yan majalisun na yankin Kudu maso Gabas sun cimma matsayar yin kira kai tsaye ga Shugaba Tinubu domin a saki Kanu ta hanyar yi masa afuwa kamar yadda jaridar The Punch ta tabbatar da labarin.

Yayin karanta sanarwar bayan taron, Idu Igariwey, dan majalisa mai wakiltar Afikpo ta Arewa da Kudu (Ebonyi), ya ce duk da cewa suna mutunta hukuncin kotu, lamarin ya wuce matakin shari’a yanzu ya koma a matsayin batu na siyasa da tsaro.

Kara karanta wannan

Kanu: Gwamna ya fara shirin ganin an saki jagoran IPOB bayan tura shi gidan yari

“Kungiyar 'yan majalisar wakilai na Kudu maso Gabas sun tattauna kan hukuncin da aka yanke wa Mazi Nnamdi Kanu da tasirinsa ga zaman lafiya da tsaro a yankin."
"Muna mutunta kotuna da tsarin shari’a, amma nauyin da ke kanmu ya sa mu yi magana idan doka ta rikide zuwa matsalar kasa mai girma da ke da tasiri kan jin kai, tattalin arziki da tsaro.”

- Idu Agariwey

'Yan majalisar Igbo na son a saki Mazi Nnamdi Kanu
Jagoran kungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu Hoto: Favour Michael Kanu
Source: Facebook

Ya kara da cewa sun yanke shawarar neman Shugaba Tinubu ya yi amfani da Sashe na 175 na Kundin Tsarin Mulki domin yi wa Kanu afuwar siyasa da ta jin kai.

'Tsare Kanu na haifar da tashin hankali'

“Ci gaba da tsare Mazi Nnamdi Kanu ya taimaka matuka wajen kara tashin hankali da rikici a yankin Kudu maso Gabas.”

- Idu Agariwey

Sun yi kira da a dauki mataki na siyasa domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, musamman ganin cewa tsare Kanu ya janyo tashe-tashen hankula, asarar rayuka, asara kan tattalin arziki da takura ga al’umma.

Shirin Gwamna Otti kan sakin Kanu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya fara shirin ganin an saki jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Iyalan Nnamdi Kano sun 'gano' makarkashiyar hallaka shi bayan tura shi Sokoto

Gwamna Otti ya bayyana cewa ya ƙaddamar da wata hanya ta siyasa da diplomasiyya domin ganin an saki Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar IPOB da aka haramta.

Hakazalika, gwamnan ya ja kunnen ’yan siyasa da su guji amfani da halin da Kanu yake ciki wajen neman biyan bukatunsu na siyasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng