Tinubu Ya Umarci Janye Ƴan Sanda da Ke Rakiyar Manya, Za a Dauki Dubban Jami'ai

Tinubu Ya Umarci Janye Ƴan Sanda da Ke Rakiyar Manya, Za a Dauki Dubban Jami'ai

  • Shugaba Bola Tinubu ya ba da sabon umarni kan jami'an yan sanda kan rakiyar manyan mutane a Najeriya
  • Tinubu ya umarci a janye dukkan ‘yan sanda daga manyan mutane nan take, a mayar da su kan aikin tsaro a yankuna
  • Gwamnati ta ce daga yanzu masu bukatar tsaro za su nemi jami’an NSCDC, yayin da Tinubu ya amince da daukar sababbin ‘yan sanda 30,000

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggawa na janye dukkan ‘yan sanda da ke tsare manyan mutane (VIPs) a fadin kasar nan.

Tinubu ya bayar da wannan doka ne yayin wani muhimmin zaman tsaro da aka yi a fadar gwamnati tare da shugaban yan sanda, hafsan sojojin kasa da na sama, da shugaban DSS.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa har yanzu ba a hukunta 'masu' daukar nauyin ta'addanci ba': Minista

Tinubu ya umarci janye yan sanda daga gadin manyan Najeriya
Bola Tinubu yayin ganawa da shugabannin tsaro a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umarnin da Tinubu ya ba yan sanda

Tinubu ya umarta a mayar da jami’an ‘yan sanda zuwa ainihin aikin su na kare al’umma a cikin yankunan da ake fama da karancin jami’ai.

A sabon tsarin, duk wani babban mutum da ke bukatar tsaro daga gwamnati zai nemi jami’an tsaron NSCDC, maimakon jami’an ‘yan sanda kamar yadda ake yi a baya.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen karfafa samar da ‘yan sanda a yankunan karkara, inda rashin jami’an tsaro ya bar jama’a cikin hadari da hare-haren ‘yan bindiga.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Yawancin yankuna, musamman kauyuka, na fama da karancin ‘yan sanda, wanda hakan ke wahalar da aikin kare rayuka da dukiyoyi.
"Shugaba Tinubu na son jami’an su maida hankali kan ainihin aikin su na ‘yan sanda.”

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

Za a sake diban sababbin yan sanda

Don karfafa sabon tsari, shugaban kasa ya amince da daukar sababbin ‘yan sanda 30,000 a fadin kasa, tare da shirye-shiryen inganta cibiyoyin horarwa cikin hadin guiwa da gwamnatocin jihohi.

Wadanda suka halarci taron sun hada da hafsan sojoji, Laftanar-janar Waidi Shaibu da na sojojin sama Air Vice Marshal, Sunday Kelvin Aneke.

Sauran sun hada da sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun da kuma daraktan DSS, Tosin Adeola Ajayi.

Fadar shugaban kasa ta ce wannan umarni wani bangare ne na sabon tsari da aka kirkiro domin karfafa jami’an tsaro da inganta tsaron al’umma a duk fadin kasar nan.

PDP ta taso Tinubu a gaba kan rashin tsaro

Kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ce rufe makarantu saboda tsaro na iya taimaka wa ’yan ta’adda, domin dama wannan ne burinsu kan Arewacin Najeriya.

Jam’iyyar ta bukaci a aiwatar da tsarin kare makarantu na kasa, tana mai cewa rufe makarantu ba zai magance matsalar ba.

Kara karanta wannan

Shugaban DSS ya fadi halin tsaron da kasa ke ciki yayin ganawa da Tinubu

PDP ta kuma zargi gwamnati da nuna halin ko in kula, inda ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus idan ba zai iya ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.