Gwamnatin Kaduna Ta Taso El Rufai a Gaba kan Zargin Biyan 'Yan Bindiga N1bn

Gwamnatin Kaduna Ta Taso El Rufai a Gaba kan Zargin Biyan 'Yan Bindiga N1bn

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya zargi gwamnatin jihar Kaduna da biyan 'yan bindiga N1bn
  • Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta fito ta yi martani mai zafi kan zarge-zargen da tsohon gwamnan ya yi
  • Ta bayyana cewa ko kadan maganganun nasa ba su da tushe kuma akwai alamun sanya siyasa a cikinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta yi martani kan zargin da tsohon gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ya yi kan cewa ta biya 'yan bindiga N1bn.

Gwamnatin ta karyata zargin na Nasir Ahmad El-Rufai, tana mai kiran ikirarin nasa a matsayin mara tushe wanda ke cike da siyasa.

Gwamnatin Kaduna ta yi wa El-Rufai martani
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna da Nasir El-Rufai Hoto: @ubasanius, @elrufai
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai zafi da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Hon. (Dr.) Sule Shu’aibu, SAN, ya fitar.

Kara karanta wannan

Ta kacame tsakanin gwamnatin Kebbi da Sanata kan matsalar tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya yi zargin ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Channels tv, inda ya ce gwamnatin Uba Sani ta biya kudin fansa ga miyagun kungiyoyi da ke aikata laifuffuka a jihar.

Wane martani gwamnati ta yi wa El-Rufai?

Gamnatin ta ce maganganun El-Rufai ba su da tushe, ba su da ma’ana kuma ba shi da wata hujja.

Sanarwar ta zargi tsohon gwamnan da kokarin ruda jama’a, tada hankalin mutane, da kuma adawa da nasarori kan tsaro da gwamnatin yanzu ta samu a jihar Kaduna.

Gwamnatin ta kuma zargi El-Rufai da yin wasa da al’amuran tsaro da rashin nuna dattaku, tana mai cewa duk wani shugaba a matakinsa, ya kamata ya yi magana cikin gaskiya da taka-tsantsan.

Gwamnatin Uba Sani ba ta biyan 'yan bindiga kudi

Sanarwar ta jaddada cewa Gwamna Uba Sani bai taɓa biyan kudin fansa ba, bai ba da izini ko amincewa da tattaunawa da ’yan bindiga ba, bai san wani ɗan bindiga ba, kuma bai taɓa ba su ko da kobo ɗaya ba.

Kara karanta wannan

Kanu: Gwamna ya fara shirin ganin an saki jagoran IPOB bayan tura shi gidan yari

Gwamnatin Kaduna ta karyata El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Har ila yau, sanarwar ta tunatar cewa Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ya taɓa karyata irin wadannan zarge-zarge da El-Rufai ya yi a baya.

Ta ce ONSA ya bayyana zargin a matsayin marasa tushe kuma ba su da alaka da gaskiyar yadda tsaro ke gudana a kasa.

Ta kuma jaddada cewa gwamnatin tarayya ba ta biyan kudin fansa ga kungiyoyin 'yan bindiga a matsayin wani tsarin gwamnati.

'Yan bindiga sun sako mutane 500 a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ta bayyana cewa ta samu nasarar kubutar da mutane 500 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Gwamnatin ta ce ta yi amfani da sabon tsarin samar da zaman lafiya wanda bai shafi biyan kudin fansa ko amfani da karfin makami kan 'yan bindiga ba.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kaduna, Ahmed Maiyaki ya ce sabon tsarin samar da tsaron ya mayar da hankali kan tattara bayanan leƙen asiri, tattaunawa, da kuma haɗa kan jama’a don samar da ci gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng