Gwamna Bago Ya Gano Masu Taimakawa 'Yan Bindiga wajen Farmakar Makarantu
- Gwamnan jihar Neja Muhammad Umaru Bago, ya kai ziyarar jaje fadar Sarkin Borgu kan daliban da 'yan bindiga suka sace
- Umar Bago ya bayyana cewa akwai maau taimakawa 'yan bindiga wajen kai hare-haren da suke kai wa a jihar
- Gwamna Bago ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa na bakin kokari domin ganin an kubutar da daliban cikin aminci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Muhammad Umaru Bago, ya ce masu bada bayanai (infomomi) na taka muhimmiyar rawa wajen bai wa ’yan ta’adda damar kai hare-hare.
Gwamna Bago ya nemi a ɗauki tsauraran matakai a kansu domin rage matsalar tsaro a jihar.

Source: Twitter
Jaridar The Guardian ta ce gwamnan ya yi wannan jawabi ne yayin ziyarar jaje da ya kai fadakar Sarkin Borgu, Alhaji Muhammad Haliru Dantoro IV, da ke New Bussa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Bago ya je ziyarar jaje
Gwamna Bago ya jagoranci tawaga daga jihar domin jajantawa kan harin da ya kai ga sace daliban makarantar St. Mary’s Catholic School, Papiri, da ke karamar hukumar Agwara.
Bago ya bayyana cewa jami’an tsaro tare da gwamnatin jihar na kokari matuka domin ganin an ceto daliban cikin gaggawa.
Ya bukaci jama’a su rika bayar da ingantattun bayanai ga jami’an tsaro, tare da jan kunnen al’umma kan nuna kiyayyar addini.
Gwamna Bago ya bayyana cewa zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummomi na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro.
Sarkin Borgu ya gode wa gwamnan bisa ziyarar, yana mai bayyana shi a matsayin shugaba mai kula da jin daɗin mutanensa.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ’yan bindiga suka mamaye gandun dajin Borgu, inda ya roki gwamnati ta tarayya da ta jiha su tserar da yankin daga hannun miyagu.
Tun da farko, karamin ministan noma, Aliyu Sabi Abdullahi, ya yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa saurin daukar matakai kan lamarin.
Ya nuna kwarin gwiwa cewa za a ceto yaran da kuma dakile ayyukan ’yan bindiga.

Source: Facebook
Gwamnatin Neja ta rufe makarantu
A matsayin martani ga sace daliban, Gwamnan Bago ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da na kudi, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da labarin.
Haka kuma ya umarci dukkan manyan makarantu da ke yankin Neja ta Arewa da sauran yankuna masu barazana a Neja ta Gabas da su dakatar da aiki har sai an bada sanarwa.
"Za mu rufe dukkan makarantun jihar Neja, firamare da sakandare, na gwamnati da masu zaman kansu har sai bayan sabuwar shekara. Makarantu a Neja ta Arewa kuma za su ci gaba da zama a rufe har sai an ba da sabuwar sanarwa."
- Gwamna Bago
Gwamnan Bago ya jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne ceton daliban da aka sace cikin koshin lafiya.
Adadin daliban da aka sace a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta bayyana adadin daliban da aka sace a jihar Neja.
Kungiyar CAN ta bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da gomman dalibai tare da wasu daga cikin malamansu zuwa cikin daji.
Ta bayyana cewa mutane 227 da suka kunshi dalibai da malamai ne 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su a harin da suka kai cikin dare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


