Babbar Magana: Gwamnatin Kebbi Ta Dauki Mataki kan Makarantu bayan Sace Dalibai

Babbar Magana: Gwamnatin Kebbi Ta Dauki Mataki kan Makarantu bayan Sace Dalibai

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta dauki matakin rufe makarantu biyo bayan harin da 'yan bindiga suka kai inda suka sace dalibai
  • Makarantun da aka rufe sun hada da na gwamnati da na masu zaman kansu da ake da su a fadin jihar
  • Gwamnatin ta sanar da shugabannin makarantun cewa za a sanar da lokacin da za a sake bude su a nan gaba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta umarci a rufe dukkan makarantun sakandare na gwamnati da na masu zaman kansu.

Hakazalika gwamnatin ta umarci rufe dukkan manyan makarantu a fadin jihar, banda kwalejin koyon aikin jinya da ke Birnin Kebbi.

Gwamnatin Kebbi ta rufe makarantu
Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu na jihar Kebbi Hoto: @NasirIdrisKIG
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta ce an bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, 23 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Ta kacame tsakanin gwamnatin Kebbi da Sanata kan matsalar tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kebbi ta rufe makarantu

Kwamishinan ilmin manyan makarantu, Alhaji Issa Abubakar-Tunga, da kwamishinar ilmin firamare da sakandare, Dr. Halima Bande, suka fitar da sanarwar tare a Birnin Kebbi, babbn birnin jihar Kebbi.

Sanarwar ta ce rufe makarantun na da nasaba da hare-haren da ’yan bindiga suka kai a wasu yankuna na jihar kwanan nan, lamarin da ya sanya ya zama dole a dauki matakin, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da labarin.

Manyan makarantu da lamarin ya shafa sun haɗa da kwalejin fasaha ta jiha da ke Dakingari, jami'ar kimiyya da fasaha ta Kebbi da ke Aliero, (KSUSTA).

Sauran sun hada da kwalejin lafiya ta kimiyya da fasaha da ke Jega da kwalejin ilmi da ke Argungu.

Sai dai rufewar ba ta shafi kwalejin koyon aikin jinya da unguwar zoma da ke Birnin Kebbi ba, wadda ita kadai ce ba a rufe ba.

Sanarwar ta bukaci mahukunta da shugabannin makarantun da lamarin ya shafa da su bi umarnin gwamnati cikin nutsuwa, tare da cewa za a sanar da sabuwar ranar komawa karatu a nan gaba.

Kara karanta wannan

Mai Mala Buni: Gwamna ya hango hadari, ya rufe dukkan makarantun kwana

'Yan bindiga sun sace dalibai

'Yan bindiga dai sun kai hari a ranar Litinin a makarantar GGCSS, Maga, da ke a karamar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi.

An rufe makarantu a jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A yayin harin, 'yan bindigan sun kashe mataimakin shugaban makarantar, Hassan Yakubu Makuku, sannan suka sace dalibai 25.

Harin ya faru ne shekaru fiye da 10 bayan sace yara mata 276 na makarantar Chibok a jihar Borno, lamarin da ya jahankalin duniya tare da haifar da shahararren gangamin #BringBackOurGirls.

Tun wancan lokacin, an ci gaba da fuskantar hare-hare da garkuwa da dalibai a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.

Iyayen yara sun tsorata

Wani mazaunin jihar Kebbi, Lukman Isa Kamba, ya shaidawa Legit Hausa cewa iyaye sun shiga halin dar-dar kan tura 'ya'yansu zuwa makaranta.

Ya bayyana cewa kulle makarantun ya yi domin matsalar rashin tsaron tana barazana ga karatun yara.

"Eh to gaskiya cikin mutane ya duri ruwa, ina ganin matakin da aka dauka na rufe makarantun ya yi daidai."

Kara karanta wannan

Matawalle ya yi bayani bayan gano wurin da aka boye 'daliban da aka sace a Kebbi

"Muna fatan dai Allah Ya kawo mana karshen matsalar, Ya kuma kubutar da yaran da aka sace."

- Lukman Isa Kamba

Gwamnatin Kebbi ta koka kan janye sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta nemi samun bayanai daga hukumomin tsaro bayan janye dakarun sojoji kafin sace dalibai.

Gwamna Nasir Idris ya bukaci sanin dalilin janye dakarun da aka tura makarantar GGCSS Maga, kafin sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar.

Nasir Idris ya ce lamarin ya tayar masa da hankali matuƙa saboda janye sojoji duk da cewa gwamnatin jihar ta bai wa jami’an tsaro rahoton sirri tun kafin faruwar harin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng