Ana Neman Daliban Kebbi, 'Yan Sanda Sun Ceto Mata 25 da Aka Yi Garkuwa da Su

Ana Neman Daliban Kebbi, 'Yan Sanda Sun Ceto Mata 25 da Aka Yi Garkuwa da Su

  • Rundunar ‘yan sanda ta ceto mata da yara 25 da aka yi garkuwa da su a Kuraje, Gusau, bayan artabu da 'yan bindiga
  • Kwamishinan ‘yan sandan Zamfara, Ibrahim Maikaba, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin da kwarewa da jarumta
  • Wannan na zuwa ne bayan ministan tsaro, Bello Matawalle, ya tabbatar da gano inda aka boye daliban Kebbi da aka sace

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ta ceto mutane 25 da suka haɗa da mata da yara da ‘yan bindiga suka sace.

An ruwaito cewa 'yan ta'addar sun yi garkuwa da mutanen ne daga kauyen Kuraje, da ke yankin Damba, karamar hukumar Gusau ta jihar.

'Yan sanda sun ceto mutane 25 da aka yi garkuwa da su a Zamfara
Wasu jami'an 'yan sanda lokacin da suka fita aiki. Hoto: @Princemoye1
Source: Twitter

Yadda aka sace mutane 25 a Zamfara

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Majalisar dinkin duniya ta shiga lamarin sace dalibai a Neja

Mai magana da yawun rundunar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a Gusau ranar Asabar, in ji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 9:45 na dare ranar Juma’a lokacin da ‘yan bindiga dauke da makamai suka mamaye kauyen, suna harbe-harbe don tsoratar da jama'a.

“Lokacin harin, ‘yan ta’addar sun sace mata goma da yara goma sha biyar, dukkansu daga Kuraje,” in ji Abubakar.

DSP Abubakar ya ce, bayan sun samu kiran gaggawa daga mazauna garin, tawagar hadin gwiwa ta ‘yan sanda da jami’an tsaorn CPG suka garzaya wajen.

An hada mutanen da aka ceto da iyalansu

Ya ce sun bi sahun ‘yan bindigar, inda aka yi artabu mai ƙarfi da su, wanda ya haifar da ceton dukkanin mutane 25 ba tare da wani ya ji rauni ba.

Bayan haka, an kai wadanda aka ceto zuwa Sabongari, Damba, domin cikakken bincike da sake haɗa su da iyalansu.

“An riga an mika matan da yaran ga iyalansu lafiya,” in ji sanarwar DSP Abubakar.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Ibrahim Maikaba, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin da kwarewa da jarumtaka, yana mai cewa hakan hujja ce ta jajircewar rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan

CAN: Dalibai da malamai 227 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a Jihar Neja

Ministan tsaro Bello Matawalle ya ce an gano inda aka boye dalibai mata na Kebbi.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Hoto: @Bellomatawalle1
Source: Original

An gano inda aka boye daliban Kebbi

A wani lamari makamancin haka, Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya tabbatar da cewa dakarun tsaro sun gano inda aka ajiye dalibai mata na makarantar Kebbi da aka sace.

A cewar rahoton Premium Times, dalibai 25 ne aka sace daga makarantar GGCSS Maga, a karamar hukumar Danko Wasagu, jihar Kebbi.

Karamin ministan tsaro, yayin ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi ranar Asabar, ya ce an samu ci gaba mai kyau tun bayan da aka tura jami’an tsaro domin ceto daliban.

“Muna dab da gano ‘yan matan nan. Mun tura jami’an tsaro da dama don rufe dukkan hanyoyi daga Kebbi zuwa Zamfara da har ma da Jamhuriyar Nijar,” in ji Matawalle.

Tinubu ya tura Matawalle zuwa Kebbi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya umarci ministan tsaro, Bello Matawalle da ya komawa Kebbi domin sa ido kan aikin ceto ɗaliban Maga.

Kara karanta wannan

An kama wasu daga cikin ƴan bindigan da suka kashe Kiristoci a Kwara? Gaskiya ta fito

Matawalle, wanda tsohon gwamnan Zamfara ne, yana jagorantar ƙoƙarin tabbatar da cewa daliban sun dawo gida lafiya bayan an sace su a makon jiya.

Tinubu dai ya dage tafiyarsa zuwa Afrika ta Kudu da Angola, yana jiran rahotanni kan harin Kwara da sace ɗaliban Kebbi domin ɗaukar matakai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com