‘Na Gaza’: Sanata a Kebbi Ya Yi Nadamar Alkawari ga ’Yan Mazabarsa Lokacin Zabe

‘Na Gaza’: Sanata a Kebbi Ya Yi Nadamar Alkawari ga ’Yan Mazabarsa Lokacin Zabe

  • Sanata daga jihar Kebbi, Garba Musa Maidoki ya bayyana bakin cikinsa kan sace dalibai a Maga, yana cewa lamarin ya taba masa zuciya
  • Ya ziyarci iyalan wadanda aka kashe da shugabannin makarantar da aka kai wa hari, tare da alkawarin cewa yaran da aka sace za su dawo gida
  • Maidoki ya ce yana jin gaza wa mutanensa, yana bayyana yadda suka dogara da shi kan batun tsaro bayan sun zaɓe shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbi - Sanata da ke wakiltar Kebbi ta Kudu, Garba Musa Maidoki ya nuna damuwa game da sace dalibai da aka yi a jihar.

Maidoki ya bayyana rashin jin dadi tare da tabbatar da cewa ya gaza kare yan mazabarsa wanda hakan ya tayar masa da hankali.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Atiku da Kwankwaso sun fadawa Tinubu matakan da ya kamata ya dauka

Sanata ya koka bayan sace dalibai a Kebbi
Sanata Garba Maidoki da ke wakiltar Kebbi ta Kudu. Hoto: Sen. Garba Musa Maidoki.
Source: Facebook

Sanata ya koka bayan sace daliban Kebbi

Sanata ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar Arise TV a jiya Asabar 22 ga watan Nuwambar inda ya jajanta kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maidoki ya ce abin da ya faru a makarantar mata da ke Maga a jihar Kebbi shi ne mafi muni a rayuwarsa wanda ya taba masa zuciya.

Ya ce suna tunanin abu na faruwa a nesa, amma wannan ya faru a cikin mazabarsa a Maga, inda suka yi alkawarin cewa za su bai wa tsaro muhimmanci idan suka ci zaɓe.

Ya ce:

“Wannan shi ne mako mafi bakin ciki a rayuwata. Lokacin da muka ji labarin sace ‘yan matan Chibok, mun ɗauka kamar wani abu ne da ya faru a nesa, tamkar tatsuniya.
Amma wannan ya faru a cikin mazabata a Maga, Jihar Kebbi, mutanen da muka tabbatar musu cewa idan mun ci zaɓe, tsaronsu zai kasance a sahun gaba.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Tinubu ya umarci Matawalle ya tattara kayansa ya koma Kebbi

Sace dalibai a Kebbi ya jawo maganganu a Najeriya
Motar makaranta da aka sace dalibai a Kebbi. Hoto: Rabilu Muhammad.
Source: Twitter

Sace dalibai: Sanata ya tabbatar da gazawarsa

Sanata Maidoki ya kuma ce ya ba su tabbacin cewa “ba za su kasance kamar ‘yan matan Chibok ba; za su dawo gida lafiya.”

Maidoki ya ce ko kadan bai ji dadi ba kuma yana jin ya gaza kare al'ummarsa da ya yi wa alkawari kafin zabe, cewar Vanguard.

“A halin yanzu, ina jin cewa na gaza wa mutanena. Mutanena sun fara kare kansu da kansu saboda rashin tsaro.
A lokacin kamfe ɗina, na nuna musu katin zaɓe na ce musu shi ne mafi ƙarfi daga cikin makaman kare kai; cewa shi ne tikitin tsaronsu. Na kuma roƙe su da su yi rajista su zaɓi mutanen da suke da mutunci waɗanda za su iya ba su tabbacin tsaro, sun ji shawara. Na lashe zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP."

Matawalle ya yi magana kan sace dalibai

Kun ji cewa Bello Matawalle ya bayyana cewa an samu ci gaba matuka a kokarin ceto daliban makarantar Maga da 'yan bindiga suka sace a Niger.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda aka wulakanta 'yan kwallon Najeriya a jirgi, an kira su 'yan ta'adda

Karamin ministan tsaron ya ce an tura dakarun sojoji zuwa iyakoki da hanyoyin da 'yan bindiga ke bi a tsakanin Kebbi, Zamfara da Niger.

Dalibai mata kusan 25 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su, amma daga bisani daya daga ciki ta gudo kuma ta koma gida.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.