Kanu: Gwamna Ya Fara Shirin Ganin an Saki Jagoran IPOB bayan Tura Shi Gidan Yari

Kanu: Gwamna Ya Fara Shirin Ganin an Saki Jagoran IPOB bayan Tura Shi Gidan Yari

  • Ana ci gaba da tafka muhawara kan hukuncin daurin rai da rai da kotu ta yankewa jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu
  • Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa yana da wani shiri na ganin cewa Kanu ya samu 'yanci duk da hukuncin da aka yanke masa
  • Hakazalika, ya ja kunnen 'yan siyasa da ke neman amfani da halin da Kanu yake ciki don cimma wata manufa ta su ta siyasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Abia - Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya ce ya ƙaddamar da wata hanya ta siyasa da diplomasiyya domin ganin an saki Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar IPOB da aka haramta.

Gwamna Otti ya bayyana hakan ne bayan da kotun tarayya ta Abuja ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai kan laifuffukan ta’addanci.

Kara karanta wannan

Iyalan Nnamdi Kano sun 'gano' makarkashiyar hallaka shi bayan tura shi Sokoto

Gwamna Alex Otti na shirin ganin an saki Nnamdi Kanu
Gwamna Alex Otti na jihar Abia da Nnamdi Kanu Hoto: @alexottiofr
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta ce hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da Gwamna Otti ya fitar a ranar Asabar, 22 ga watan Nuwamban 2025.

A ranar 20 ga watan Nuwamba ne mai shari’a Justice James Omotosho ya samu Nnamdi Kanu da laifi a tuhume-tuhumen ta’addanci, inda ya yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

Wane shiri Gwamna Otti ke yi kan Kanu

Gwamna Otti ya bayyana cewa wannan dabarar ta musamman da suke amfani da ita don ganin an saki Kanu ta fara ne tun a farkon shari’ar.

Ya ce yana farin cikin sanar da jama’a cewa yana ci gaba da bin tsarin da suka tsara tare da manyan jami’an gwamnati har sai an cimma burin ganin an sake shi, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar da labarin.

Gwamna Otti ya ce a baya ya ziyarci Kanu a inda aka tsare shi, inda ya shaida masa ci gaban tattaunawar da ake yi da “manyan hukumomi” a matakin kasa, bisa tsarin da aka yarje kafin nan.

Kara karanta wannan

An yi yunkurin kashe alkalin da ya daure Nnamdi Kanu? Kotun tarayya ta magantu

“Duk da cewa Mazi Nnamdi Kanu na da ’yancin daukaka kara kan hukuncin, ina farin cikin sanar da ku cewa na kaddamar da tsarin da muka amince da shi tun farko, kuma zan ci gaba da bin sa har sai mun kai ga samun ’yancinsa.”

- Gwamna Alex Otti

Otti ya soki yadda aka tafiyar da batun IPOB

Gwamnan ya ce yadda aka tafiyar da batun IPOB tun daga kan tushe ne ya haifar da matsalolin da ake fuskanta yanzu, don haka ba za a bar lamarin ya yi tsawo ba har ya rikide zuwa wata babbar barazana.

Ya kuma gargadi ’yan siyasa da su guji amfani da halin da Kanu yake ciki wajen neman biyan bukatunsu na siyasa, yana bayyana cewa hakan na iya lalata yunkurin da ake yi na magance matsalar.

“Ina jan kunnen ’yan siyasa da suke son amfani da halin da Mazi Nnamdi Kanu yake ciki su guji hakan, su haɗa kai da mu domin ganin an sake shi.”

- Gwamna Alex Otti

Gwamna Otti ya soki yadda aka tafiyar da batun IPOB
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti Hoto: @alexottiofr
Source: Facebook

Gwamna Otti ya roki jama'a

Gwamnan ya roki jama’ar Abia da ma daukacin yankin Kudu maso Gabas da su kwantar da hankalinsu, su guji maganganun da za su iya cutar da tattaunawar diplomasiya da ake yi yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya sanya ranar fara azumi, addu'o'i, ya shawarci Musulmi, Kirista

Otti ya ce zai ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki da sauran ’yan Najeriya masu kishin kasa domin bin hanyar siyasa da diplomasiyya, don warware matsalar tare da gwamnatin tarayya.

Batun shirin hallaka Kanu

A wani labarin kuma, kun ji cewa iyalan jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, sun mika kokensu gaban kasashen duniya.

Iyalan na Nnamdi Kanu sun yi zargin cewa akwai shirin hallaka shi bayan babbar kotu ta yanke masa hukuncin rai da rai.

Kanin jagoran na IPOB, Emmanuel Kanu, ya bayyana cewa sauya masa wurin zama daga ofishin DSS zuwa gidan gyaran hali na Sokoto na kunshe da makircin hallaka shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng