Facebook Ya Sauke Shafin Fasto da Ya Ke Ikirarin Kashe Kiristoci, an Fara Tunzura
- Mutane da dama sun fara korafi bayan tabbatar da cewa an goge shafin Facebook na Fasto da yake ikirarin kisan Kiristoci wanda ya tayar da kura
- Fasto Ezekiel Dachomo da kansa ya tabbatar da haka ga wasu manema labarai lamarin da ya fara jawo ce-ce-ku-ce musamman tsakanin masoyansa
- Dachomo ya shahara da ya bayyana cewa ya gudanar da jana’izar gawarwaki sama da 67, tare da gabatar da shaida a gaban Majalisar Amurka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Al'umma da dama sun fara korafi bayan tabbatar da sauke shafin Facebook na fitaccen Fasto a Najeriya.
Fasto Ezekiel Dachomo na daga cikin malaman da suka fara yada kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci a Najeriya wanda ya dauki hankalin duniya.

Source: Facebook
An roki bude shafin Facebook na Fasto

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka, Trump ya kara daukar zafi, ya kira Najeriya da kalma mara dadin ji
Wani matashin Fasto a Najeriya, Evang Peter Otene ya tura roko na musamman wanda ya wallafa a Facebook domin ganin an dawo da shafin Dachomo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Otene ya roki Facebook da ta dawo da shafin Dachoma duba da irin gudunmawar da yake ba al'umma musamman bayan zargin kisan Kiristoci.
Ya ce Dachomo ba wai kawai mai wa'azi ba ne, ya kasance mutum mai karfin zuciya da yake iya magana kan cin zarafin addini da ake yi a Arewacin Najeriya.
Fasto ya tabbatar da kulle shafinsa na Facebook
Fasto Ezekiel Dachomo daga Plateau ya bayyana cewa an share shafinsa na Facebook gaba daya.
Ya tabbatar da hakan ga Daily Post lokacin da aka tuntube shi a ranar Asabar 22 ga watan Nuwambar 2025 da muke ciki.
Lokacin da aka tambaye shi ko shafin nasa an goge shi, Dachomo ya ce a takaitaccen zance da cewa:
"Eh, Gaskiya ne.”

Source: Facebook
Zargin Fasto da ya jawo magana a Najeriya
Wannan na faruwa ne a lokacin da maganganunsa game da kisan Kiristoci ke jawo mahawara inda wasu ke ganin ya wuce gona da iri.

Kara karanta wannan
Sace dalibai: An taso Tinubu a gaba, malami ya buƙace shi don Allah ya yi murabus
Dachomo kwanan nan ya yi hira da Piers Morgan inda ya ce ya yi fiye da jana’izar gawarwaki s67 saboda hare-haren da ake kaiwa al’ummomi a Najeriya.
Ya kuma gabatar da shaida a Majalisar Dokokin Amurka kan lamarin domin tabbatar da abin da yake fada, kamar yadda Sahara Repoter ta ruwaito.
An kuma tuna cewa Shugaba Donald Trump ya sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ke fuskantar barazana ta addini inda ya ce zai iya daukar matakin soji kan kasar.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce alkaluman da Trump ya dogara da su kuskure ne kuma ba su nuna ainihin gaskiya ba.
Fasto ya umarci iyalinsa idan aka sace shi
Kun ji cewa malamin addini a jihar Plateau ya yi magana kan masu garkuwa da mutane inda ya yi wa mabiyansa gargadi kan biyan kudin fansa.
Fasto Ezekiel Dachomo ya ce idan an sace shi, kada a biya fansa, yana mai cewa jininsa zai haifar da yaki na ’yantar da Kiristoci.
Malamin ya bayyana cewa ya yarda da haɗarin da yake ciki game da kisan gilla a Arewa, musamman waɗanda ke kai wa Kiristoci hari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng