'Yan Bindiga Sun Nemi N3bn kan Daliban da Suka Sace a Neja? An Ji Gaskiyar Zance

'Yan Bindiga Sun Nemi N3bn kan Daliban da Suka Sace a Neja? An Ji Gaskiyar Zance

  • An yada wasu rahotanni masu ikirarin cewa 'yan bindiga sun nemi kudin fansa har N3bn kan daliban da suka sace a Neja
  • Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Neja ta fito ta warware zare da abawa kan batun neman kudin fansar
  • Hakazalika, kungiyar CAN ta musanta cewa makarantar ta samu rahoton tsaro kan yiwuwar kawo harin 'yan bindiga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen jihar Neja, ta yi martani kan rahotannin cewa 'yan bindiga sun nemi kudin fansa kan daliban da suka sace.

Kungiyar CAN ta karyata rahotannin cewa 'yan bindigan sun nemi N3bn a matsayin kudin fansa kan dalibai da malamai 315 da suka sace daga St. Mary’s Catholic Primary and Secondary Schools, da ke Papiri a karamar hukumar Agwara.

CAN ta yi martani kan neman kudin fansar daliban Neja
Tambarin kungiyar CAN da allon makarantar St Mary a Neja Hoto: @CANmedia/@DanKatsina50
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta ce shugaban CAN na jihar, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna, wanda shi ne Bishop na Diocese na Kontagora, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 22 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

"Akwai wata a kasa": Sheikh Ahmad Gumi ya hango manufar sace dalibai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne yayin da yake bada sababbin bayanai kan sace daliban da 'yan bindigan suka yi.

Meye gaskiyar batun kudin fansa?

A cewarsa, masu garkuwa da mutanen har yanzu ba su tuntubi kowa ba bayan sace mutanen.

“Kun san halin kafafen sada zumunta. Idan ka shiga can, za su iya karkatar da kai. Wasu abubuwan da ake yadawa ba daidai ba ne. Shi ya sa muke fitar da bayanai a hukumance. Ni ban san hakan ba. Babu wani kira tukuna.”

- Bulus Dauwa Yohanna

Mutane nawa aka sace a makarantar?

A baya, Bishof Bulus ya tabbatar cewa adadin wadanda aka sace ya kai mutum 315. Binciken da suka sake yi ya nuna cewa dalibai 303 da malamai 12 ne aka dauke.

“Bayan mun bar makarantar Papiri, sai muka yi kira, muka sake tantancewa, muka kuma bincika wadanda muka yi tunanin sun tsere. A nan muka gano cewa wasu dalibai 88 da suka yi kokarin tserewa an kama su.”

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Majalisar dinkin duniya ta shiga lamarin sace dalibai a Neja

- Bulus Dauwa Yohanna

Ya ce hankalinsu ya tashi ne bayan wasu iyaye da aka yi zaton ‘ya’yansu sun tsere sun dawo suna tambayar su, wanda hakan ya sa aka sake kididdiga, inda aka gano cewa suna cikin wadanda aka sace.

Wannan ya tabbatar da cewa waɗanda aka sace sun haɗa da, dalibai 303 (maza da mata), malamai 12 (mata hudu da maza takwas), inda aka samu jimillar mutane 315, rahoton jaridar The Punch ta zo da labarin.

Ya kuma bayyana cewa adadin daliban makarantar kafin harin ya kai 629, inda firamare ke da 430, sannan sakandare ke da 199.

Kungiyar CAN ta musanta batun neman kudin fansa
Taswirar jihar Neja, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Batun kin bin umarnin gwamnati

Bishof Yohanna ya kuma yi karin haske kan rahotannin da ake yadawa cewa an samu rahotannin tsaro kafin harin.

“Ba gaskiya ba ne. Ba mu samu wata takarda ko sanarwa daga gwamnati ba. Wannan kawai ƙoƙari ne na sauya magana."
"A baya, a shekarar 2022, idan mun ji jita-jitar barazana, nan take muke rufe makaranta. Shin yanzu kuma sai gwamnati ta fitar da sanarwa mu ki bi?”

Kara karanta wannan

CAN: Dalibai da malamai 227 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a Jihar Neja

- Bulus Dauwa Yohanna

Majalisar dinkin duniya ta yi Allah wadai

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dinkin duniya ta yi magana kan sace dalibai da 'yan bindiga suka yi a jihar Neja.

Majalisar dinkin duniya ta yi Allah wadai da harin na 'yan bindiga wanda ya ritsa da dalibai da malamansu.

Ta bukaci hukumomi da su gaggauta daukar matakan da suka dace domin ganin cewa an kubutar da daliban cikin koshin lafiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng