Abu Ya Girma: Majalisar Dinkin Duniya Ta Shiga Lamarin Sace Dalibai a Neja
- Majalisar Dinkin Duniya ta yi magana kan harin da 'yan bindiga suka kai a jihar Neja inda suka yi awon gaba da wasu dalibai
- Mai magana da yawun majalisar ya yi Allah wadai da harin wanda ya bayyana a matsayin abin da ke girgiza zuciya
- Stéphane Dujarric ya yi nuni da cewa harin na zuwa ne bayan an yi wani makamancinsa a Kebbi, aka yi awon gaba da dalibai mata
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da sace ɗaruruwan ɗalibai da malamai da aka yi a jihar Neja.
'Yan bindiga dai sun sace daliban ne a makarantar St. Mary’s Catholic Primary and Secondary School da ke jihar Neja a ranar Juma’a, 21 ga watan Nuwamban 2025.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce mai magana da yawun majalisar dinkin duniya, Stéphane Dujarric, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Stephen Dujarric ya bayyana harin a matsayin 'abin girgiza zuciya', yana mai jaddada cewa wajibi ne makarantu su kasance wuraren da yara ke karatu cikin tsaro inji jaridar Vanguard.
'Yan bindiga sun sace dalibai a makarantu
Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan makamancin sace-sacen da aka yi na dalibai a jihar Kebbi.
A ranar Litinin, ’yan bindiga sun sace akalla dalibai 25 tare da kashe wani malami a harin da suka kai makarantar GGCSS, Maga, a Kebbi.
A cewar kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ’yan bindiga sun sace dalibai 215 da malamai 12 daga makarantar da ke Papiri, karamar hukumar Agwara a jihar Neja.
Me majalisar dinkin duniya ta ce?
“Mun sake fuskantar wani hari na sace ɗalibai a jihar Neja, ’yan kwanaki bayan sace yara 'yan makaranta a Kebbi.”
“Muna tare da wakilin UNICEF da majalisar dinkin duniya a Najeriya, Mohamed Malick Fall, wajen nuna tausayinmu ga iyalai da al’ummomin da abin ya rutsa da su."

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai
"Dole yanzu ya kamata dukkan kokari ya mayar da hankali kan dawo da yaran cikin gaggawa da koshin lafiya.”
- Stephane Dujarric
Dujarric ya jaddada cewa yawaitar irin wadannan hare-hare na kara nuna gaggawar da ake da ita wajen aiwatar da tsarin 'Safe Schools'.
A cewarsa tsarin ya kunshi matakai na musamman domin kare makarantu da tabbatar da damar yara su ci gaba da karatu ko da a lokacin rikici.

Source: Twitter
Gwamnati ta rufe makarantu
Bayan sace-sacen, gwamnatin tarayya ta sanar da rufe makarantun kwana 41 na Federal Unity Colleges.
Ma’aikatar llimi ta tarayya ta bayyana a wata takarda ranar Juma’a cewa wannan mataki ya samo asali ne daga tsanantar matsalolin tsaro, kuma an yi shi ne domin kare rayuka da hana sake faruwar irin wadannan hare-hare.
Jam'iyyar ADC ta ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa ta ba shugaban kasa, Bola Tinubu, shawara bayan fasa tafiya zuwa kasashen waje sabosa sace dalibai.
Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa ya kamata shugaban kasar ya je jihar Kebbi biyo bayan sace daliban da 'yan bindiga suka yi.
Ta nuna cewa soke tafiyar da Tinubu ya yi ba wani abu ba ne face wasan kwaikwayo na siyasa don nuna ya damu kan lamarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

