Karfin Hali: 'Yan Bindiga Sun Nemi Kudin Fansa har Naira Biliyan 3 a Kwara

Karfin Hali: 'Yan Bindiga Sun Nemi Kudin Fansa har Naira Biliyan 3 a Kwara

  • ’Yan bindiga sun nemi kudin fansa Naira miliyan 100 ga kowane mutum daga cikin masu ibadar da suka sace a cocin CAC, Eruku
  • A kalla mutane 30 zuwa 35 aka yi garkuwa da su yayin harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku a wani yanki na jihar Kwara
  • Biyo bayan lamarin, matasa sun gudanar da zanga-zanga, yayin da gwamnan jihar ya nemi karin matakan tsaro a yankin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - Al’umma a yankin Eruku da ke cikin karamar hukumar Ekiti ta jihar Kwara sun shiga firgici bayan harin da ’yan bindiga suka kai cocin CAC a lokacin da ake gudanar da ibada.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutane tsakanin 30 zuwa 35, lamarin da ya sake tayar da hankalin jama’a a yankin kan tabarbarewar tsaro.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake shiga makaranta sun sace dalibai da malamai a Neja

Wasu 'yan bindiga a Najeriya
Wasu 'yan bindiga suna taro. Hoto: Zagazola Makama
Source: Twitter

Rahoton Channels TV ya nuna cewa wani mutum a Eruku, Olusegun Olukotun, ya ce ’yan bindigar sun fara kiran iyalan wadanda aka sace domin neman kudin fansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun ce suna bukatar Naira miliyan 100 ga kowane mutum.

Ya kara da cewa shi da wani daga cikin iyalansa sun tsere ta taga yayin da harin ya fara, amma sauran danginsa hudu suna hannun ’yan bindigan.

'Yan bindiga na neman kudin fansa N3bn

Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindigar sun kai harin ne a wani taron ibada da aka yi, inda suka shafe kusan sa’a guda suna cin karensu babu babbaka.

Cif Olukotun ya bayyana cewa masu garkuwar sun raba wadanda suka sace zuwa rukuni-rukuni bisa ga dangantakarsu, sannan suka fara kiran iyalai ta kowanne rukuni kan kudin fansa.

Ya ce har yanzu bai samu kiran da ya shafi danginsa ba, amma wasu mazauna yankin sun riga sun ji kira daga ’yan bindigan suna neman Naira miliyan 100 a kan kowane mutum guda.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Matasa 16 da suka gama digiri sun mutu a hanyar zuwa sansanin NYSC

Idan aka yi jimillar kudin da suke nema a kan kowa da kowa, kudin zai kai N3bn ko ya wuce haka.

Martanin cocin da zanga zanga da aka yi

Faston cocin, Abiodun Bamidele, ya ce mutane kusan 30 zuwa 35 ne aka sace, yana mai bayyana cewa suna gudanar da wani taro ne abin ya faru.

Wannan ya sa matasan Eruku suka fantsama zanga-zanga, suka toshe babban titin Ilorin–Kabba, lamarin da ya haifar da cinkoso mai yawa.

Matasa sun zargi jami’an tsaro da kasa mayar da martani a kan lokaci duk da kasancewar akwai jami’an tsaro a yankin.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq. Hoto: Kwara State Government
Source: Facebook

Shugaban matasa, Peter Adesiyan, ya soki ’yan sanda, yana cewa duk da taimakon da al’umma suka ba sashen ’yan sanda wajen wasu tsare-tsare, ba su kai dauki ba a kan lokaci ba.

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya nemi karin tura jami’an tsaro cikin gaggawa a yankin domin dakile sababbin hare-haren da ke ta kunno kai, musamman a kan iyakokin jihar.

An sace dalibai a jihar Neja

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun sace dalibai a wata makaranta.

Kara karanta wannan

Saukar farashi: Yadda manoma ke tafka asara bayan girbi a daminar bana

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga makarantar ne cikin dare yayin da dalibai da malamai ke barci.

Gwamna Umaru Bago ya ce an ba jami'an tsaro umarnin gaggawa domin ceto daliban da aka sace a makarantar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng