"Ba Ƴan Ta'adda ba ne": An Gano Ƴan Bindigan da Suka Kai Hari Jihar Kano

"Ba Ƴan Ta'adda ba ne": An Gano Ƴan Bindigan da Suka Kai Hari Jihar Kano

  • Mazauna karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano sun kwana a cikin firgici bayan bakon al'amari na harin 'yan bindiga ya same su
  • Sai dai tuni tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafe na jihar, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce ba 'yan ta'adda ba ne
  • Ya yi karin bayani a kan harin, inda ya ce ba irin 'yan bindigan da ke kutsawa garuruwa suna kwashe mutane ana garkuwa da su ba ne

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Ana cigaba da zaman tsoro a yankin Rimin Gado na jihar Kano bayan wani mummunan lamari da ya faru a daren Alhamis a kauyen Gulu.

Wadansu mutane da aka yi fargabar 'yan bindiga ne sun shiga garin wanda ya tayar da hankulan mazauna yankin har zuwa safiyar Juma’a.

Kara karanta wannan

Bayan kashe Kiristoci a coci, ƴan bindiga sun sake kai hari Kwara, sun sace mutane

'Yan bindiga sun kai hari Kano
Kwamishinan 'yan sandan Kano, Ibrahim Bakori, Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa/Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Amma a karin bayani da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafen jama'a a jihar, Muhiuyi Magaji Rimin Gado ya ce ba 'yan ta'adda ba ne.

'Yan bindiga sun kai hari Kano

Barista Muhuyi Magagi Rimin Gado, bayyana cewa mutanen da su ka kai hari garinsa, wato Rimin Gado, 'yan fashi ne ba 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane ba.

Yan fashi sun sace kudi a kasuwar kauyen Kano
Taswirar jihar Kano, inda 'yan ta'adda suka kai hari Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce:

"Babu wani harin 'yan ta'adda (masu garkuwa da mutane a Gulu). Illa dai 'yan fashi da babura biyu sun kai hari garin. Jami'an tsaro na kokarin cafke su.'

Wani mazaunin yankin, Hamza Haruna Gulu, ya tabbatar majiyar Legit da faruwar harin, inda ya bayyana cewa maharan sun shigo kauyen ne misalin 8.00 na dare a ranar Alhamis.

Ya ce ana zargin barayi kimanin huɗu zuwa shida ne suka fara bude wuta a kasuwar garin, lamarin da ya jefa mutane cikin firgici da gudun neman tsira.

Kara karanta wannan

Me ke faruwa? Fusatattun matasa sun rufe babban titi a Arewa, sun hana kowa wucewa

Ya kara da cewa maharan sun nufi shagon wani 'dan kasuwa, Malam Isa Mai Dusa, inda suka sake harbe-harbe sannan suka shiga shagon suka kwashe kuɗin da suka tarar.

Hamza ya ce har zuwa safiyar Juma’a babu jami’an tsaro da suka isa wurin, abin da ya ƙara tsorata jama’a.

Mazauna kauyen Kano sun koka

Hamza Haruna Gulu kara da cewa rabonsu da ofishin 'yan sanda a yankin tun shekaru kusan 30 da suka gabata, kuma yanzu suna zaune babu jami'an tsaro ko a kusa.

Saboda haka, ya roki gwamnati ta gaggauta dawo da ofishin domin kare jama’a da dukiyoyinsu. Ya kuma tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa duk da harbe-harben da aka yi.

Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin shugaban karamar hukumar Rimin Gado, Muhammad Sani Salisu Jili, domin ya yi bayanin matakan da ake dauka, amma bai samu haɗa waya da shi ba.

Gwamnan Kano ya tashi game da tsaro

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Jihar Kano ta ƙara zage dantse wajen tabbatar da tsaro a fadin jihar, inda gwamna Abba Kabir Yusuf ya mikawa rundunar JTF sababbin kayan aiki.

Kara karanta wannan

Ana jimamin sace dalibai a Kebbi, 'yan bindiga sun yi ta'asa a Sokoto

Wannan na kunshe a cikin wani jawabin mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa,ya fitar inda ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin inganta tsaro a Kano.

A cikin kayan da aka rabawa jami’an, akwai sababbin motoci 10 da babura 50 da za su taimaka wajen yaki da laifuffuka da kuma faɗaɗa damar kai daukin gaggawa idan abu ya faru.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng