'Abin da Ya Hana Tinubu zuwa Kebbi bayan Sace Dalibai Mata'

'Abin da Ya Hana Tinubu zuwa Kebbi bayan Sace Dalibai Mata'

  • 'Yan bindiga sun kai hari a wata makarantar sakandiren kwana da ke jihar Kebbi inda suka yi awon gaba da wasu dalibai
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai samu zuwa jihar ba domin jajantawa kan aika-aikar da 'yan bindigan suka yi
  • Sanata Uzor Orji Kalu ya bayyana dalilin da ya sanya shugaban kasan bai je jihar Kebbi da kansa ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana dalilin da ya sa Shugaba Bola Tinubu, bai je jihar Kebbi ba.

Sanata Kalu ya ce hukumomin tsaro ne suka hana Shugaba Tinubu tafiya zuwa jihar Kebbi bayan sace dalibai 25 na makarantar GGCSS Maga.

Kalu ya fadi dalilin Tinubu na kin zuwa Kebbi
Sanata Uzor Orji Kalu da shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu Hoto: Senator Uzor Orji Kalu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

Sanata Kalu ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Tinubu ya umarci Matawalle ya tattara kayansa ya koma Kebbi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Shugaba Tinubu bai je Kebbi ba?

Ya ce shugaban kasa ya shirya zuwa Kebbi, amma hukumomin tsaro suka ba shi shawarar kada ya tafi saboda dalilan tsaro.

“Shugaban kasa yana shirin zuwa Kebbi, amma jami’an tsaro suka dakatar da shi, suka ce mataimakin shugaban kasa ya je.”

- Sanata Uzor Orji Kalu

Sanata Kalu ya ce mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ziyarci Kebbi a madadin Tinubu, ya kuma dawo ya ba shi rahoto.

Tsohon gwamnan na Abia ya kara da cewa Shugaba Tinubu ya soke wasu muhimman ayyuka da ya tsara a Afrika ta Kudu, Angola, da wasu kasashe domin ci gaba da zama a Abuja.

Ya ce shugaban kasan ya zauna gida ne domin jimamin mutanen da suka rasu a harin da aka kai cocin da ke jihar Kwara, da kuma gudanar da muhimman tarurruka da manyan hafsoshin tsaro.

Kalu ya ce Tinubu ya damu kan hare-hare

Kara karanta wannan

Kiraye kiraye sun yawaita, ana son Tinubu ya yi murabus daga shugabancin Najeriya

Sanata Kalu ya ce Shugaba Tinubu ya kasance cikin damuwa sosai tun bayan samun labarin abin da ya faru a Kebbi da Kwara, yana mai cewa 'yan majalisu ma sun nuna irin wannan damuwar.

Sanata Kalu ya yi magana kan Tinubu
Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar dattawa, Uzor Orji Kalu Hoto: Senator Uzor Orji Kalu
Source: Facebook

Ya ce Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya soke wani taro da ya shirya domin komawa jam’iyyar APC saboda irin waɗannan munanan al’amura da ake fuskanta.

“Don haka Shugaba Tinubu ya nuna jagoranci; ya nuna damuwa, ya nuna kulawar uba ga ’ya’yan da aka sace a Kebbi, kuma haka ya kamata.”

- Sanata Uzor Orji Kalu

Jigon na APC ya nuna kwarin gwiwa cewa Najeriya za ta shawo kan matsalolin da take fuskanta a halin yanzu.

Maganar Sanatan Amurka kan sace dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Jim Rich mai wakiltar Idaho a majalisar dattawan Amurka, ya yi magana kan sace daliban da 'yan bindiga suka yi a jihar Kebbi.

Sanata Jim Risch ya zargi gwamnatin tarayya da gazawa wajen kare yara masu zuwa makaranta daga hare-haren mayakan jihadi da 'yan ta'adda.

Hakazalika, Risch ya bayyana cewa daliban makaranta, musamman ’yan mata sun zama wadanda ake kai wa harin don yin bautar dole, tilasta canza addini ko kuma neman kuɗin fansa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng