'Yan Bindiga Sun Buga Ta'asa a Sokoto, An Kashe Mutane kuma An Sace Jarirai
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun sake kai wani harin ta'addanci kan bayin Allah a wani kauyen jihar Sokoto
- Tsagerun 'yan bindigan sun kai farmakin ne cikin dare a kauyen Kurawa da ke karamar hukumar Sabon Birni
- Harin ya jawo an hallaka mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane ciki har da mata masu shayarwa da jariransu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - ’Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kauyen Kurawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
'Yan bindigan sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da mutane 15, ciki har da wasu mata huɗu masu shayarwa da jariransu.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa maharan wadanda aka ce sun zo dauke da makamai masu karfi sun farmaki kauyen ne kusan karfe 11:30 na dare.

Kara karanta wannan
Bayan kashe Kiristoci a coci, ƴan bindiga sun sake kai hari Kwara, sun sace mutane
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto
Daga cikin wadanda suka rasu akwai wani jigo a cikin al’umma mai suna Alhaji ISU Saraki.
Wasu mutum biyu kuma, ciki har da wani jami’in rundunar tsaro ta jihar Sokoto, sun samu raunuka inda suke karɓar magani a asibiti.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, ɗan majalisar da ke wakiltar yankin, Hon. Sa’idu Ibrahim, ya ce mutum 15 ne maharan suka tafi da su.
“Wadanda aka sace sun hada da mata shida, hudu daga cikinsu masu shayarwa ne. An kuma tafi da jariransu, tare da matasa biyar masu shekaru tsakanin 14 da 15.”
- Hon. Saidu Ibrahim
Meyasa 'yan bindiga ke kai hare-hare?
Hon. Saidu Ibrahim ya danganta karuwar hare-haren yankin da farmakin da sojoji ke kai wa a Zamfara da kuma shirin sulhu a Katsina, wanda ya ce ba zai yi nasara ba domin 'yan bindiga ba su da niyyar mika makamai.
Ya kuma bayyana cewa duk da cewa an dawo da jami’an ’yan sandan Mopol zuwa yankin, ba su zama a wuraren da aka tura su yadda ya kamata.
Harin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan wani hari a kauyen Tarah, wanda maharan suka yi garkuwa da mutane tara tare da jikkata mutum guda.

Source: Original
A wancan lokacin, an ce ’yan sa-kai na yankin an mayar da su zuwa Katsina, abin da ya bar kauyen Tarah babu tsaro.
Mazauna yankin sun ce matasa sun yi gaggawar tunkarar maharan, abin da ya hana 'yan ta'addan tafka gagarumar barna.
Wadannan hare-haren sun kara tayar da hankalin jama’a game da yawaitar garkuwa da mutane da kashe-kashen da ke aukuwa a yankin, duk da ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro.
'Yan bindiga sun kai hari a Kwara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani kauye da ke masarautar Lafiagi ta jihar Kwara.
'Yan bindigan sun yi sun yi garkuwa da manoma hudu a harin da suka kai masu lokacin suna aikin girbi a gonakin shinkafa da yammacin ranar Laraba.
Mazauna yankin sun bayyana cewa 'yan bindigan sun mamaye garin a bazata, suka yi wa manoman kawanya yayin da suke tattara shinkafar da suka girbe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

