Magana Ta Kare: Kotu Ta Yankewa Nnamdi Kanu Hukunci bayan Samunsa da Laifi

Magana Ta Kare: Kotu Ta Yankewa Nnamdi Kanu Hukunci bayan Samunsa da Laifi

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke hukunci a shari'ar gwamnati da jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu
  • Alkalin kotun, mai shari'a James Omotosho ya samu Kanu da laifi a dukkanin tuhume-tuhume bakwai da ake yi masa
  • James Omotosho ya yankewa babban wanda ake zargi hukuncin daurin shekara 20 a gidan gyaran hali kan tuhuma ta biyu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kotu ta yanke hukunci ga jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu, hukunci kan zargin aikata ta'addanci.

Kotun da ke zama a birnin Abuja ta yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai, bayan ta same shi da laifin ta’addanci.

Kotu ta yankewa Nnamdi Kanu hukunci
Jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a kotu Hoto: @ImranMuhdz
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta kawo rahoton cewa alkalin kotun, mai shari'a James Omotosho ne ya sanar da hukuncin ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

A karshe, kotu ta kama Nnamdi Kanu da laifin ta'addanci, ta yanke masa hukunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta samu Nnamdi Kanu da laifi

Mai shari'a James Omotosho ya yanke hukuncin ne a ranar Alhamis, shekara huɗu bayan kama Nnamdi Kanu a Kenya cikin yanayi mai cike da cece-kuce, aka kuma dawo da shi Najeriya.

Daga nan aka gurfanar da shi a kan tuhume-tuhume bakwai da suka shafi ta’addanci.

Jaridar Vanguard ta ce an yanke hukuncin ne ba tare da Kanu ya halarta ba, domin ya dage cewa ba za a yanke hukunci a shari’ar ta’addancin da gwamnatin tarayya ta shigar a kansa ba.

Sakamakon hayaniyar da ta kaure a kotu, alkalin ya umurci jami’an tsaro su fitar da shi daga zauren kotu saboda ɓata tsarin zaman kotu.

Omotosho ya bayyana cewa kalaman Kanu a Radio Biafra sun kunshi ayyukan ta’addanci, yana mai cewa kalamansa da manufarsa duk sun ta’allaka ne kan tashin hankali.

Alkalin ya kara da cewa umarnin zama a gida da Kanu ya bayar a jihohin Kudu maso Gabas shi ma aiki ne na ta’addanci, saboda ya tauye wa mutanen yankin ’yancin zirga-zirga.

Kara karanta wannan

Ba fashi: Alkali zai yankewa Nnamdi Kanu hukunci bayan fitar da shi daga harabar kotu

Kotu ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga Kanu
Jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu Hoto: Favour Michael Kanu
Source: Facebook

Mai shari'a Omotosho ya tabbatar da cewa Kanu bai da wani iko a kundin tsarin mulki da zai ba shi damar ya umurci jama’a da su zauna a gida.

A cewarsa, daga bayanan da ke gaban kotu, Kanu ya yi shirin aiwatar da ta’addanci ta hanyar jawabansa inda ya ba da umarnin kashe jami’an ’yan sanda da na sojoji.

Kotun ta bayyana cewa shugaban na IPOB ya aikata ta’addanci kan jamhuriyar rarayyar Najeriya.

An same shi da laifi kan dukkan tuhume-tuhume bakwai, duk da cewa ya ce bai amince da laifukan da ake tuhumarsa da su.

Wane hukunci kotu ta yankewa Kanu?

Mai shari'a James Omotosho ya yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai kan tuhume-tuhume na hudu, biyar da na shida daga cikin tuhume-tuhume bakwai da ake masa.

Hakazalika kotun ta yanke masa hukuncin shekaru 20 a gidan yari kan tuhuma ta biyu da ake masa.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: 'Yan majalisa 44 sun tura wasika ga Tinubu kan sakin shugaban IPOB

Yadda aka shirya yanke wa Kanu hukunci

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta shirya zartar da hukunci kan shari'ar da ake yi wa Nnamdi Kanu.

Alkalin kotun, mai shari'a James Omotosho, ya bayyana cewa zai yanke hukuncin ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamban 2025.

Sai dai, Kanu ya dage cewa ba za a cigaba da zama ba saboda a cewarsa bai kammala shigar da jawabansa na karshe ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng