‘Kai Makaryaci ne’: Yar Siyasar Canada Ta Zagi Ministan Tinubu, Ya Yi Martani Mai Zafi
- An yi rigima yayin da Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar ya musanta zargin cewa ana kisan Kiristoci da gan-gan a Najeriya.
- Wata tsohuwar ‘yar majalisar Canada ta zargi Najeriya da boye gaskiya, tana kiran kashe-kashen da “Jihadi”, lamarin da Tuggar ya kira jahilci
- Tuggar ya ce bayanan da ake yadawa kan adadin Kiristocin da aka kashe ba gaskiya ba ne, yana zargin Ghamari da neman raba ƙasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya yi muhawara mai zafi da tsohuwar ‘yar majalisar Canada, Goldie Ghamari.
Yan siyasar sun ta jifan juna da kalamai marasa dadi da zubar da mutunci yayin muhawara kan zargin kisan Kiristoci.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani bidiyo a shirin Piers Morgan Uncensored wanda aka wallafa a Youtube kan zargin kisan Kiristoci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta'addanci: Yar Canada ta zargi gwamnatin Najeriya
Ghamari ta zargi gwamnati da mara wa hare-haren Boko Haram da ISWAP baya, tana kiran lamarin “Jihadi”, tana cewa gwamnati tana ɓoye adadin mutanen da ake kashewa.
Ta ce hare-haren da ake kai wa Kiristoci, ciki har da na Chibok, suna nuna yunkurin yaƙi na addini, tana amfani da tarihi wajen goyon bayan kalamanta.
Tuggar ya mayar da martani da cewa bayananta jahilci ne kuma masu haɗari, yana cewa ƙarya ake yadawa kan mutanen da suka mutu cikin shekaru 10 da suka wuce.
Ministan ya bayyana cewa rikicin Libya bayan kisan Muammar Gaddafi ne ya haifar da yawaitar makamai, da dagula tsaro a Najeriya da ƙasashen yanki.
Ghamari ta kara zargin cewa shugabancin kasar bai da wakilcin Kirista, tana cewa Ministan yana guje wa haka idanu da ita saboda “ƙaryarsa” game da gaskiyar kashe-kashe.

Source: Twitter
'Ainihin yawan Kiristoci da aka kashe' - Minista
Tuggar ya dakatar da ita, yana cewa gwamnatin ba ta rarrabe waɗanda suka mutu ta addini ba, kuma bayanai kan yawan Kiristoci 177 da ya bayar sun fito daga hukumomin tsaro.
Piers Morgan ya tambayi dalilin ministan na sauya kalamai, amma Ministan ya ce akwai bayanai, sai dai ba a ware su bisa addini saboda tsarin kundin Najeriya.
Tuggar ya bayyana cewa shi ma ya rasa surkinsa da yan uwa a harin yan ta’adda, yana jaddada cewa Musulmai da ba su goyon bayan Boko Haram ne suka fi fuskantar hare-haren su.
Ghamari ta ci gaba da zargi, tana cewa sojoji suna ba Fulani damar kai hari, tana kira Ministan “jahili”, da cewa akwai “kisan gillar Kiristoci”.
Tuggar ya maida martani da zafi, yana zargin Ghamari da neman kuɗi wurin yada fargaba da wargaza ƙasashe, yana cewa ta bar Najeriya ta huta.
Ambasada Tuggar ya yi ikirarin an jawo rugajewar kasashe irinsu Sudan kuma a yanzu an nufo Najeriya.
CAN ta yi maraba da matakin Trump
An ji cewa kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN ta yi maraba da matakin da Shugaba Donald Trump na Amurka ke shirin dauka a kasar.
Shugaban kungiyar, Rabaran Daniel Okoh, ya yi magana kan zargin kisan Kiristoci da ake yi a ƙasar inda ya tabbatar ana kashe su.
Okoh ya ce suna maraba da shawarar Amurka na taimaka wa Najeriya wajen kawo ƙarshen kashe-kashe da rashin tsaro a ƙasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


