Majalisar Dattawa Ta Yi Magana da Allah Ya Yi Wa Sanata Rasuwa a cikin Dare
- Ana ci gaba da tura sakon alhini da ta'aziyya bisa rasuwar Sanata mai wakiltar Enugu ta Arewa, Okechukwu Ezea na jam'iyyar LP
- Majalisar dattawa ta bayyana jimamin wannan babban rashi, tana mai cewa marigayin ya ba da gudummuwa mai yawa a fannin dokoki
- Ta mika sakon ta'aziyya ga al'ummar mazabar Enugu ta Arewa, gwamnatin Enugu, da iyalansa tare da addu'ar Allah ya ji kan Sanata Ezea
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawa ta bayyana alhini kan rasuwar Sanata Okechukwu Ezea (LP, Enugu ta Arewa), wanda ya rasu a daren Talata, 18 ga Nuwamba, 2025.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dattawa, Sanata Adeyemi Adaramodu, ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Source: Facebook
Ya ce Najeriya ta yi babban rashi, domin marigayin yana daga cikin manyan ’yan majalisar dattawa da ke aiki a halin yanzu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar bayanin da iyalinsa suka fitar, Sanata Ezea ya rasu ne a asibiti mai zaman kansa a Legas, misalin ƙarfe 11:07 na dare, bayan gajeriyar rashin lafiya.
Majalisa ta jero alheran Sanata Ezea
Da yake mika sakon ta'aziyya a madadin majalisar, Adeyemi ya ce marigayi Sanata Ezea, wanda ya lashe zaben 2023 a inuwar LP, ya kasance mai tasiri a Majalisar Dattawa ta 10.
"A farkon majalisar ta 10 a 2023, ya shugabanci Kwamitin Ladabtarwa, Hakkoki da Korafe-korafe, kafin daga bisani ya koma jagorancin wasu manyan kwamitoci.
"Har zuwa lokacin rasuwarsa, shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Hulɗa da Ci gaban Afirka da NEPAD kuma Mataimakin Shugaban Kwamitin Al’adu da Tattalin Arzikin Zamani.
"Ezea ya bar gado mai tasiri ta fuskar dokoki da muhawara a majalisa. Daga cikin manyan kudurorinsa akwai kafa Kwalejin Noma ta Tarayya, Adani, Kudirin kafa Jihar Adada."
Har ila yau, Sanata Adeyemi ya ce marigayin shi ne ya gabatar da kudirin da ya nemi a kafa sansanin soji a Karamar Hukumar Uzo-Uwani domin dakile hare-haren ’yan bindiga a yankin.
Majalisar Dattawa ta mika sakon ta'aziyya
A karshe dai Majalisar Dattawa ta ce tana mika sakon ta’aziyya ga al’ummar mazabar Enugu ta Arewa, gwamnatin jihar Enugu, da iyalan mamacin da kasa baki daya.
Ta kuma bayyana cewa Najeriya ta yi babban rashin mutum mai hangen nesa da taimakon al'umma, inda ta yi addu'ar Allah ya j ikan sa, in ji Leadership.
“Mun yi babban rashi, muna roƙon Allah Ya jikansa, Ya ba shi hutu madawwami," in ji Sanata Adeyemi Adaramodu.

Source: Facebook
Dan Agbese ya riga mu gidan gaskiya
A baya, kun ji labarin cewa babban dan jarida a Najeriya, Dan Agbese ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 81 da haihuwa.
Agbese ya shahara wajen rubuce-rubuce masu tasiri kuma ya shafe shekaru masu ɗimbin yawa yana ba da gudunmawa a aikin jarida tun daga 1980.
Ana ganin dai rasuwarsa za ta bar babban gibi a harkar jarida, musamman ga waɗanda suka san shi a matsayin jagora kuma jajirtaccen edita.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

