An Kashe Shanu kusan 300 a Mummunan Hari kan Makiyaya a Benue

An Kashe Shanu kusan 300 a Mummunan Hari kan Makiyaya a Benue

  • An kashe akalla shanu 259 a hare-haren da aka kai wa makiyaya a Benue, lamarin da ake ganin yana iya tayar da sabon faɗa a jihar
  • Wasu makiyaya sun ce wasu kungiyoyin tsaron yankuna ne da ake zargin suna samun goyon bayan wasu mahukunta ke kai harin
  • Shugabannin makiyaya a yankin sun yi gargadin cewa halin shiru daga hukumomi na iya zama wata barazana da za ta tayar da rikici

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Tashin hankali ya fara kunno kai a jihar Benue bayan jerin hare-hare da aka kai wa al’ummomin makiyaya wanda ya kai ga kashe shanu fiye da 250.

Lamarin ya faru a yankunan Gwer ta Yamma da Guma, kuma rahotanni sun nuna cewa abin na iya haifar da sake rikicewar kabilu idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba.

Kara karanta wannan

Wasu dalibai mata da aka sace a Kebbi sun kubuta daga hannun 'yan bindiga

Wasu shanun da aka kashe a Benue
Shanun da aka kashe a Benue a cikin ruwa. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa rahotanni daga filin da lamarin ya faru sun bayyana cewa wasu mutane dauke da makamai ne suka kai hari sau biyu a rana guda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu rahotanni daga shaidu sun ce an ga waɗanda suka kai harin suna shagali da gawar shanun a tsakiyar gari.

Hargin farko da aka kai kan makiyaya

Harin farko ya faru ne a kusa da yankin Naka, inda masu kai harin suka tare makiyayan da ke kiwo a wajen.

Abdullahi Musa ya ce an kashe masa shanu 50, yayin da Wakili Musa ya bayyana cewa shanu 51 aka hallaka masa.

Wani makiyayi, Maibargo Abubakar kuwa ya ce an kashe masa 21 ba tare da wani tarzoma daga bangarensu ba.

Wasu shaidu sun bayyana cewa:

“Harin wani gangami ne da aka yi da gangan domin tada rikicin kabilanci.”

An ce maharan sun kwashe gawar shanun zuwa cikin Naka, inda aka gansu cikin farin ciki, abin da ya kara tada hankalin al’umma.

Kara karanta wannan

Bayan kashe Janar a Borno, an hallaka wani jami'in sojan Najeriya a Legas

Hari na 2 da aka kai wa makiyayan

Bayan Gwer, an kai wani hari a bayan ƙauyen Okohol, kusa da Ikpam, cikin karamar hukumar Guma. A nan ne aka kashe shanu 137 mallakar Alhaji Anaruwa Yongo da dan uwansa.

Bayanai da suka fito sun ce an kwashe wasu gawarwakin shanun, sannan wasu kuma aka bar su a filin kiwo.

Wata saniya da aka kashe a Benue
Wata saniya da aka kashe a harin da aka kai Benue. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Majiyoyin tsaro da suka ziyarci wuraren bayan faruwar lamarin sun tabbatar da ganin gawar shanun, amma har yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro ko gwamnati.

Zarge-zargen da makiyaya ke yi

Shugabannin makiyaya sun bayyana cewa irin wannan hari abu ne da ake maimaitawa a jihohi kamar Enugu, Neja da Kebbi.

Sun zargi wasu hukumomin yankin da “bada tallafi ga ƙungiyoyin da ke kai hari kan makiyaya” tare da yin shiru idan an samu ramuwar gayya.

Makiyayan sun ce duk da rahotanni da suka sha bayyanawa da sunayen masu laifi, ba a ɗauki matakin hana irin wadannan hare-haren a Benue ba.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun fitar da matsaya kan daliban Kebbi da aka sace

Yadda aka kai hari kan dalibai a Kebbi

A wani labarin, kun ji cewa wasu da suka kasance a kusa da makarantar GGSS Maga da aka sace dalibai sun fadi yadda abin ya faru.

Wani shaidan gani da ido ya ce maharan sun iso marantar ne da asuba yayin da jama'a ke shirin fitowa sallah.

Ya kara da cewa daga zuwansu suka fara harbi ba kakkautawa kafin su samu damar shiga makarantar su sace dalibai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng