Ran APC Ya Baci, Ta Dura kan PDP saboda Neman Taimakon Trump a Najeriya
- Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nuna bacin ranta game da kalaman shugaban PDP a kasar kan kiran Amurka
- APC ta soki kira da shugaban PDP ya yi na neman kasashen waje su shiga lamurran Najeriya, tana mai cewa hakan rashin kishi ne
- Ta bayyana Tanimu Turaki a matsayin shugaba rudadde wanda bai san hanyar magance matsalolin jam’iyyarsa ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Bisa ga dukkan alamu kalaman sabon shugaban PDP a Najeriya, Kabiru Tanimu Turaki ya fusata jam'iyyar APC mai mulki.
Jam’iyyar APC ta soki kiran da shugaban yan adawa a PDP, Tanimu Turaki, ya yi na neman kasashen waje su shiga cikin harkokin Najeriya.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da APC ta wallafa a yau Talata 18 ga watan Nuwambar 2025 a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta roki Amurka ta ceci siyasar Najeriya
Turaki, yayin ganawa da ’yan jarida a Abuja game da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyarsa, ya ce ana bukatar agajin kasashen waje.
Ya bukaci Amurka ta taimaka domin hana abin da ya kira “kisan ƙare-dangi na Kiristoci” da kuma kare dimokuradiyya a ƙasar nan.
Wannan kira da PDP ta yi ya jawo maganganu da ra'ayoyi mabambanta duba da halin da ake ciki yanzu bayan barazanar Amurka.
Martanin APC ga PDP bayan neman taimakon Amurka
A cikin sanarwar, jam'iyyar mai mulki ta ce wannan kira kwata-kwata babu tunani a ciki kuma rashin kishin ƙasa.
A martanin da ta fitar, kakakin APC na ƙasa, Felix Morka, ya yi Allah-wadai da wannan magana, yana mai cewa PDP ta yi abin kunya tare da yin kira mai hatsari ga kasar.
Ya ce Turaki ya riga ya nuna alamun rashin dabara da rudani wajen magance rikicin cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan
"Ba kisan kiristoci kadai ake ba," Turaki ya bukaci Amurka ta kawo dauki Najeriya

Source: Twitter
'Abin da ake tsammanin shugaban PDP zai nema'
Morka ya ce ’yan Najeriya sun yi tsammanin Turaki zai fara neman zaman lafiya a jam’iyyarsu ta PDP, ta hanyar hada kan bangarori masu rikici domin samar da mafita.
Amma abin farko da ya yi shi ne yin kira da kasashen waje su mamaye Najeriya, wanda APC ta bayyana a matsayin maganar rashin kunya kuma barazana ga tsaron kasa da mutuncinta.
A cewar APC, ko a lokacin mulkin PDP na shekaru 16, duk da yadda ta danne jam’iyyun adawa, ba a taba jin wani ya yi kiran harin kasashen waje domin magance rikicin jam’iyya ba.
Ta ce wannan kira daya ne daga cikin alamu masu nuna cewa PDP ta kasa magance matsalolinta kuma hakan ya nuna ta kai ga karshen karafinta.
Jam’iyyar ta bukaci kasashen duniya da su yi watsi da kiran PDP, tana mai cewa wannan yunkuri ne kawai domin tayar da kura ta siyasa.

Kara karanta wannan
Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'
Jiga-jigan PDP sun ba hamatta iska a Abuja
An ji cewa rikici ya barke tsakanin bangarorin jam’iyyar PDP a hedikwatar jam’iyyar bayan hatsaniya ta barke a taron ake gudanar wa a Abuja.
Jami'an tsaro sun yi yunkurin hana gwamna Bala Mohammed da Ministan Abuja, Nyesom Wike, su taron da bangarensu ya kira a Wadata Plaza.
Lamarin rikicin ya samo asali ne daga dakatar da bangaren Wike a Babban Taron Kasa na PDP da ya gudana a karshen mako.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
