Kebbi: Abin da Ya Faru kafin Ƴan Bindiga Su Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta

Kebbi: Abin da Ya Faru kafin Ƴan Bindiga Su Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta

  • Matar marigayi mataimakin shugaban makarantar Maga a Kebbi ya bayyana yadda farmakin ’yan bindiga ya faru
  • Mijin nata ya fuskanci maharan domin kare yaran, inda suka kashe shi yayin da al'umma ke kuka da kira ga gwamnati ta kare makarantu da malamai
  • Hakan ya biyo bayan sace dalibai har guda 25 a jihar Kebbi da yan bindiga suka yi wanda ya tayar da hankali

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbi - Matar marigayi mataimakin shugaban makaranta a Kebbi ta fadi yadda harin yan bindiga ya afku.

Matar mai suna Amina Hassan ta tuna yadda mummunan farmakin ’yan bindigan ya faru da safiyar Litinin, 17 ga Nuwamba, 2025.

An bayyana yadda yan bindiga suka hallaka mataimakin shugaban makaranta a Kebbi
Gungun yan ta'adda da wata mota a makarantar da aka sace dalibai a Kebbi. Hoto: Amnesty International Zagazola Makama.
Source: Facebook

Yadda marigayin ya yi kokarin kare dalibai

Rahoton Leadership ya ce harin ya kai ga garkuwa da ɗalibai mata 25 tare da kashe Mallam Hassan Yakubu.

Kara karanta wannan

Gwamna Kefas ya dakatar da shirin shiga jam'iyyar APC, ya fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi suka ce marigayin ya tsaya tsayin daka domin kare dalibansa kafin rasa ransa a lamarin.

Amina ta ce ranar ta fara babu wata matsala, cikin bazata sai ta ji karar harbe-harbe da ihun jama’a da suka ta da hankalin gidansu da unguwarsu.

Ta ce ta leƙa waje saboda jin motsi, sai ta hangi maharan dauke da bindigogi suna nufo ta, hakan ya sa ta juya da gaggawa cikin tsananin tsoro.

Ta ce:

“Sun yi barazanar kashe mijina idan ya yi wani abu dabam. Mijina ya roƙe su da su bar shi ya yi sallah kafin su kashe shi, suka yarda, suka harbe shi bayan ya gama addu’arsa ta ƙarshe.
"Lokacin da na yi ƙoƙarin matsowa kusa da gawarsa, sai suka yi barazanar kashe ni ma idan na kusanci mijina.”
An samu bayanai kan yadda aka sace ɗalibai 25 a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi da ke fama da matsalar tsaro kamar sauran jihohi. Hoto: Legit.
Source: Original

Rokon da dalibai suka yiwa matar marigayin

Ta bayyana yadda ta shige gida ba tare da gyale ko takalma ba, tana kuka, tana umartar ’yan makarantar da su ɓuya domin tsira daga harin yan bindiga.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'

Daliban sun roƙe ta ka da ta fita waje saboda tsoron maharan, ta ce maharan sun rufe gidan gaba ɗaya suna yawo da bindigoginsu cikin firgici.

A lokacin ne mijinta, Mallam Hassan, ya fuskanci ’yan bindigan domin kare yaran, abin da ya jawo suka kashe shi a nan take, cewar rahoton DW Hausa.

Kisan malam Hassan da sace ɗalibai ya kara fusata al’umma, wadanda ke kira ga kariya mai ƙarfi ga makarantu da malamai musamman a yankunan karkara.

Hukumomin tsaro sun kaddamar da bincike da aikin ceto, yayin da iyalai da jama’a ke addua don kubutar da dukkan ’yan matan da aka sace lafiya.

Shugaban sojoji ya ziyarci jihar Kebbi

Kun ji cewa babban hafsan sojojin kasan Najeriya ya isa Jihar Kebbi domin duba yiwuwar ceto daliban GGCSS Maga da aka sace har guda 25.

Shugaban sojojin ya umarci dakarun kasar su kasance a bakin aiki da farautar 'yan ta'adda domin ceto 'yan yaran da aka sace ba tare da bata lokaci ba.

Ya jaddada muhimmancin hadin kai da ‘yan sa-kai wajen kawo karshen barazanar 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane a yankunan da dama.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.