Abin da Hafsan Sojoji Ya Fadawa Dakarunsa bayan Sace Dalibai 25 a Kebbi

Abin da Hafsan Sojoji Ya Fadawa Dakarunsa bayan Sace Dalibai 25 a Kebbi

  • Babban Hafsan Sojoji, Manjo Janar Waidi Shaibu, ya yi magana ga dakarun sojoji bayan sace daliban sakandare a jihar Kebbi
  • Janar Shaibu ya umarci sojojin Operation FANSAN YANMA su tashi tsaye wajen ceto daliban GGCSS Maga da aka dauke
  • Shugaban sojojin ya ziyarci yankin, inda ya bukaci sojoji su yi aiki dare da rana ba tare da kasala ba, sannan su yi amfani da sahihin bayanai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbi - Hafsan sojojin kasa, Manjo Janar Waidi Shaibu, ya ja hankalin dakarun sojoji game da sace dalibai har guda 25 a jihar Kebbi.

Shaibu ya umurci sojojin Operation FANSAN YANMA da su yi aiki tukuru wajen neman daliban GGCSS Maga.

Shugaban sojoji ya karawa dakaru karfin guiwa bayan sace dalibai a Kebbi
Shugaban sojojin Najeriya, Waidi Shaibu da dakarunsa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Shaibu ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara jihar Kebbi bayan sace dalibai mata da aka yi a jihar, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda yan bindiga suka sace dalibai

Hakan ya biyo bayan da yan bindiga dauke da ke dauke da miyagun makamai suka kashe mataimakin shugaban makarantar mata ta GGCSS, Maga.

An ce 'yan ta'addan sun kai hari makarantar kwanan ne a daren Lahadi 16 ga watan Nuwambar 2025 inda suka sace dalibai mata masu tarin yawa.

Wata mata da lamarin ya faru a kusa da su, ta bayyana yadda maharan suka shafe awanni suna cin karensu ba babbaka.

Daliban Kebbi: Abin da hafsan sojoji ya ce

Yayin ziyararsa Jihar Kebbi, Shaibu ya bukaci sojoji su tsananta aiki dare da rana har sai an ceto dukkan ’yan matan da aka sace cikin koshin lafiya, Punch ta ruwaito.

Ya gudanar da wani zaman aiki tare da kwamandojin gaba daya kafin ya gana da sojojin da ke sintiri, yana tunasar da su cewa nasara na bukatar jajircewa na gaske.

“Dole ku ci gaba da fafatawa dare da rana. Dole mu nemo waɗannan yara."

Kara karanta wannan

Gwamnan Kebbi ya daukarwa iyayen yaran da aka sace alkawari

- Waidi Shaibu

Shugaban sojoji ya ba dakaru umarni kan sace dalibai a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi da aka sace dalibai mata 25. Hoto: Legit.
Source: Original

Jan kunnen da hafsan sojoji ya yi

Ya kara jan kunne kwamandoji su yi amfani da bayanan leken asiri, yana mai cewa ’yan bindiga kan kai hari wuraren da suka fi rauni, kuma sojoji na iya kayar da su idan sun fuskance su.

Shaibu ya ce ana bukatar kwazo da bin ka’ida lokacin samun bayanan gaggawa, domin aikin ya shafi ingancin rundunar da kare rayukan ’yan kasa baki ɗaya.

Ya kuma gudanar da wata ganawa ta musamman da 'yan sa-kai da mafarauta da ke taimakawa sojoji, yana neman hadin kai domin tabbatar da cewa an kubutar da daliban lafiya.

Gwamna ya yi alkawari ga iyayen yara

Mun ba ku labarin cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da wasu dalibai mata na wata makarantar sakandire a jihar Kebbi.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kai ziyarar gani da ido zuwa makarantar da lamarin ya auku domin ganewa idonsa halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka mamaye GGCSS Maga da harbi kafin sace dalibai mata a Kebbi

Nasir Idris wanda ya gana da iyayen yaran da aka sace, ya ba su tabbacin cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin 'ya'yansu sun kubuta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.