Obasanjo Ya Ajiye Girma Ya Kaure da Cacar Baki da Tsohon Gwamna Fayose

Obasanjo Ya Ajiye Girma Ya Kaure da Cacar Baki da Tsohon Gwamna Fayose

  • Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya sake raddi mai zafi ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
  • Fitinar da ke tsakaninsu ta sake tashi ne kwana biyu bayan sun nuna alamar sasanci a bikin zagayowar ranar haihuwar Fayose
  • Fayose ya aika sakon godiya mai dauke da zarge-zarge da kalamai masu tsanani ga Obasanjo, wanda ya mayar da martani

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sabon rikici ya sake tashi tsakanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose.

Hakan na zuwa ne duk da cewa kwanaki biyu kacal kenan da alamu suka nuna sun sasanta a bainar jama’a.

Olusegun Obasanjo da Ayo Fayose
Obasanjo da Fayose da suke rigima da juna. Hoto: @OyoNews1
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa lamarin ya samo asali ne daga martanin da Fayose ya aikawa Obasanjo ta sakon waya, wanda ya kunshi kalamai masu tsauri da zarge-zarge.

Kara karanta wannan

Alaka ta yi tsami tsakanin Tinubu da Yahaya Bello? An ji gaskiyar zance

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar Obasanjo yayin taya Fayose murna

A yayin da ya ke jawabi a taron ranar haihuwar tsohon gwamnan a ranar Asabar, Obasanjo ya tuna cewa Fayose ya sha tura mutane domin neman sulhu da shi.

Obasanjo ya ce,

“Ba kai ne mafi nagarta a yarana na siyasa ba, amma ka yi abubuwan da ba za a iya kawar da kai a kansu ba.”

Obasanjo ya kuma bayyana yadda Fayose ya tuntube shi ta hannun Osita Chidoka kafin ya yarda ya zo wajen taron.

Ya kara da cewa matakin Fayose da matarsa wajen neman afuwa ya sa ya karbi gayyatar da suka yi masa, Obasanjo ya ce ya yafe masa.

A wurin taron Fayose bai ce komai ba, abin da ya sa jama’a tunanin sulhu ya tabbata tsakaninsu, amma bayan kwana biyu kacal, ya bude wutan raddi cikin sakon godiya ga Obasanjo.

Sakon raddi da Fayose ya tura wa Obasanjo

Kara karanta wannan

'Mutane da yawa sun mutu,' Tinubu ya dauki muhimmin alkawari ga al'ummar Filato

Punch ta wallafa cewa a ranar Litinin, Fayose ya turo sakon godiya amma cikin kalamai masu tayar da kura.

Obasanjo da Atiku Abubakar
Obasanjo tare da tsohon mataimakinsa a wani taro. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

A cewar bayanin da mai magana da yawun Obasanjo, Kehinde Akinyemi ya fitar, sakon Fayose ya kunshi cin fuska da zarge-zarge masu tsauri.

A cikin sakon, Fayose ya rubuta cewa:

“Baba Obasanjo, na gode, sai dai babu dattaku a kalamanka. Ban yi mamaki ba...”

Ya ci gaba da cewa ya yi shiru a wurin taron ne:

“Domin mutane su ga bambanci tsakanin mai hankali da wanda ya ke akasin haka.”

Fayose ya kuma zargi Obasanjo da cutar mantuwa, tare da cewa zai fito ya fayyace gaskiya daga baya. Ya kuma nemi Obasanjo ya mayar masa da kudinsa.

Martanin Obasanjo ga Ayo Fayose

Bayan karanta sakon tsohon gwamnan, Olusegun Obasanjo ya mayar da amsa cikin takaitaccen sakon da ya caccaki hali da dabi’ar Fayose.

Ya ce:

“Wannan sakon naka ya nuna kai wanene — mutum mai halayya maras kyau, ba za ka canza ba.”

Ya ce ya maida kudin Fayose ta hanyar mutumin da ya kawo masa su a baya, ba tare da bude jakar ba balle ya dauki wani abu a ciki.

Kara karanta wannan

Abduljabbar: Sowore ya fadi abin da ya sa ake tsare da malamin, ya sha alwashi

Obasanjo ya ce dimokuradiyya ta mutu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi wa shugabanni nasiha kan mulki da gaskiya.

Ya koka da cewa dimokuradiyya na fuskantar barazana a fadin Afrika saboda rashin tashin shugabanni tsaye.

Obasanjo ya bayyana haka ne yayin wani taron dimokuradiyya da gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a kasar Ghana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng