Bayan Kashe Janar a Borno, an Hallaka Wani Jami'in Sojan Najeriya a Legas
- Sojan runduna ta 81 a jihar Legas ya rasu bayan wani mai tabin hankali ya kai masa hari da sandar katako a Ikorodu
- Lamarin ya faru ne yayin da sojan ke kokarin kwantar da tarzoma a yankin Imota, ranar 16 ga watan Nuwamba, 2025
- Rundunar soji ta yi ta’aziyya ga iyalan mamacin tare da bayyana cewa bincike yana gudana kan abin da ya faru
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta karɓi rahotanni da wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta game da mutuwar soja a yankin Ikorodu na jihar Lagos.
Rundunar ta ce duk da cewa ana cigaba da bincike, akwai bukatar bayyana wasu muhimman bayanai game da yadda lamarin ya faru.

Source: Original
Legit Hausa ta tattaro bayanan da rundunar sojin Najeriya ta yi ne a wani sako da ta wallafa a wani shafinta na X.
Yaushe aka kashe soja a Legas?
A cewar rundunar, lamarin ya auku ne ranar 16, Nuwamba, 2025, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, lokacin da wani soja a yankin Imota yake kokarin dakile rikici.
Yayin wannan yunkuri, wani mutum da aka bayyana a matsayin wanda bai da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa ya kai masa mummunan hari.
Rundunar ta ce wannan mutum ya buge sojan da sandar katako mai nauyi a kai, abin da ya jawo masa munanan raunuka kafin a kai shi asibiti.
An kashe wanda ya farmaki soja a Legas
Bayan kai harin, wasu daga cikin sojojin da ke wurin suka yi gaggawar mamaye wajen tare da kashe mutumin da ya kai harin domin kare sauran jama’a.
Haka kuma, sun karbi bindigar sojan sannan aka garzaya da shi zuwa Asibitin Ikorodu, inda aka tabbatar da rasuwarsa.

Kara karanta wannan
Abin takaici: Yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar majalisar tarayya a Zamfara
Daga nan aka yi masa jana’iza bisa tsarin musulunci, tare da halartar mukarraban rundunar da kuma kwamandan rundunar.
Sojoji sun yi ta'aziyyar rasuwar sojan
Rundunar sojojin ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan soja, abokai da sauran wadanda mutuwarsa ta shafa.
Ta ce tana addu’ar samun rahamar Allah ga mamacin tare da yabawa da sadaukarwarsa ga kasa a lokacin rayuwarsa.

Source: Facebook
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa an kafa kwamiti domin gudanar da cikakken bincike game da abin da ya faru.
A cikin sanarwar, rundunar ta yi kira ga jama’a da su rika bayar da rahoto kan duk wani abin da ya ke iya zama barazana ga tsaro.
Haka kuma, ta roki kafafen yada labarai da su rika yin labari cikin taka-tsantsan, domin kaucewa yada bayanai kafin kammala bincike.
An baza sojoji kan yunkurin kashe soja
A wani rahoton, kun ji cewa an baza karin jami'an tsaro a Abuja yayin da aka yada zargin cewa an yi yunkurin kashe A.M Yerima.
A ranar Lahadi ne wani lamari ya faru da sojan a birnin tarayya Abuja, inda aka ce wasu motoci sun bi Laftanan din a kan hanya.
A makon da ya wuce ne jami'in sojan ruwan Najeriya, A.M Yerima ya yi sabani da ministan Abuja, Nyesom Wike kan shiga wani fili.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

