Harajin Shigo da Mai: Matatar Ɗangote Ta Fadi Dalilin Rage Farashin Litar Fetur

Harajin Shigo da Mai: Matatar Ɗangote Ta Fadi Dalilin Rage Farashin Litar Fetur

  • Matatar Dangote ta karyata rade-radin cewa raguwar farashin fetur ta samo asali ne daga cire harajin shigo da kaya na gwamnati
  • Kamfanin ya fadi ainihin dalilin da ya jawo saukar farashin litar man Dangote a ranar 6 ga Nuwamba 2025
  • Dangote ya soki shigo da fetur mai ƙarancin inganci daga ƙasashen waje, yana cewa hakan na lalata harkar cikin gida

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Matatar mai ta Dangote ta musanta rahotannin da ke cewa ta rage kudin man fetur saboda gwamnatin ta dakatar da harajin shigo da man fetur da dizal na 15%.

A cewar kamfanin, wannan zargi ba shi da tushe, kuma ya sabawa gaskiyar abin da ke faruwa a kasuwar mai da har ya jawo aka samu sauƙin farashi.

Kara karanta wannan

Naira tiriliyan 1.4 sun yi ƙafa a CBN, an taso gwamnan babban banki ya yi bayani

Dangote ya fadi dalilin rage farashin man fetur
Hoton Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Ɗangote Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Dangote ya bayyana cewa abu ɗaya da ya haddasa wannan saukar farashi, inda aka samu ragin 5.6% da kamfanin ya yi a farashin mai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya fadi dalilin ragin farashin mai

Jaridar Punch ta wallafa cewa a ranar 6 ga Nuwamba, 2025 ne matatar ta sanar da rage farashin man fetur a jaridun Najeriya.

A cikin bayanin, kamfanin ya bayyana cewa ya rage farashin daga N877 zuwa N828 kowace lita, yayin da farashin da ake dauko shi ya sauka daga N854 zuwa N806.

Sai dai yanzu ana danganta wannan saukar farashin da dakatar da harajin shigo da kaya, abin da kamfanin ya ce kuskure ne kuma ya yaudari jama’a.

Dangote ya kuma bayyana cewa harajin 15% da ake magana a kai tun tuni ya samu amincewar shugaban ƙasa a ranar 21 ga Oktoba.

Matatar Dangote ta magantu kan farashin mai

Kara karanta wannan

'Fetur zai rage kudi': IPMAN ta fadi yadda Dangote zai sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya

Kamfanin Dangote ya ce ko an aiwatar da harajin shigo da mai ko akasin haka, ba shi da tasiri ga tsarin farashin da kamfanin yake yi.

Matatar Dangote ta ce ta taimaka wa ƴan Najeriya
Fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Kamfanin ya ce har yanzu ana cigaba da shigo da mai mara nganci daga ƙasashen waje da farashi mai tsada da ke cutar da kasa da ababen hawa.

Ya bayyana cewa shigowar matatarsa cikin tsarin sayar da mai ya taimaka wajen daidaita farashi da samar da shi cikin sauki a sassan kasar.

Kamfanin ya roki ‘yan kasuwa da kafafen yada labarai su rika wallafa bayanai na gaskiya da aka tabbatar, domin amfanin jama’ar Najeriya.

Matatar Dangote ta rage farashin mai

A baya, mun wallafa cewa matatar mai ta Dangote ta tabbatar da cewa ta rage farashin litar mai daga N877 zuwa N828 domin saukaka wa ƴan Najeriya.

A cewar bayanan da matatar ta fitar, sabon farashin ya fara aiki daga ranar 7 ga Nuwamba 2025, kuma an sa rai hakan zai kawo sauki ga masu motoci.

Rahotanni sun tabbatar da cewa rage farashin da aka yi daga N877 zuwa N828 na nufin an rage N49 a kowace lita ga masu saye kai tsaye daga matatar.

Kara karanta wannan

Bankin Duniya: Shirin gwamnatin Tinubu bai tabuka komai wajen ragewa talaka radadin fatara ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng