Lokaci Ya Yi: Fitaccen Dan Jarida a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Babban dan jarida a Najeriya, Dan Agbese ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 81 da haihuwa
- Iyalan marigayin sun tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da suka fitar yau Litinin, 12 ga watan Nuwamba, 2025
- Dan Agbese ya shafe shekaru masu yawa ya na ba da gudummuwa a harkar jarida kuma yana daya daga cikin wadanda suka kafa Newswatch
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue, Nigeria - Ɗaya daga cikin fitattun ’yan jarida kuma mamallakin jaridar Newswatch, Dan Agbese, ya rasu yana da shekara 81.
Majiyoyi daga iyalansa sun tabbatar da cewa mashahurin marubucin kuma edita ya rasu da safiyar Litinin, 17 ga Nuwamba 2025, a birnin Legas.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Agbese ya shahara wajen rubuce-rubuce masu tasiri kuma ya shafe shekaru masu ɗimbin yawa yana ba da gudunmawa a aikin jarida tun daga 1980.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da rasuwar Dan Agbese
A wata sanarwa da iyalan Agbese na Ikpilogwu, Agila, da ke karamar hukumar Ado ta jihar Benue suka fitar, sun ce:
"Muna sanar da rasuwar mijinmu, ubanmu, kakanmu, ɗan’uwanmu kuma jagoranmu, Cif Dan Agbese, Awan’Otun na masarautar Agila.”
“Cif Agbese ya tafi ya barmu da safiyar Litinin, 17 ga Nuwamba 2025. Ya na da shekara 81, za a sanar da shirye-shiryen jana’izarsa daga baya.”
Takaitaccen bayani kan dan jaridan
An haifi Agbese a ranar 12 ga Mayu 1944, a Agila, kuma ya shahara ne a matsayin gogaggen ɗan jarida kuma marubuci, wanda ya yi fice a salon rubutu mai tasiri da yake yi a jaridu da mujallu daban-daban.
Ya yi aiki a matsayin edita a The Nigeria Standard da New Nigerian, sannan ya rike matsayin shugaban gidan radiyon jihar Benuwai watau, 'Radio Benue' da ke Makurdi.
Agbese na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa mujallar Newswatch wacce ta kawo juyin juya hali a aikin jarida. Ya kasance babban edita na mujallar har zuwa Afrilu 2010.
Ya kuma yi rubuce-rubuce na littattafai masu yawa, sannan ya riƙa rubuta makaloli na yau da kullum a jaridun Daily Trust da The Guardian.

Source: Facebook
Marigayin ya kuma gudanar da kamfanin bada shawara kan harkokin yada labarai tare da abokansa Ray Ekpu, Yakubu Muhammed da Soji Akinrinade.
Dan Agbese ya mutu ya bar matarsa, Cif Rose Agbese, da ’ya’ya shida, da jikoki bakwai.
Ana ganin dai rasuwarsa za ta bar babban gibi a harkar jarida, musamman ga waɗanda suka san shi a matsayin jagora, jajirtaccen edita da ya ba da gagarumar gudunmawa ga ci gaban aikin jarida a Najeriya.
Limamin cocin Katolika ya mutu a Taraba
A wani labarin, kun ji cewa daya daga cikin manyan limaman cocin Katolika ta Wukari a Jihar Taraba, Fasto Nicholas Kyukyundu ya mutu.
Sanarwar mutuwan ta fito ne daga bakin shugaban cocin, Rabaran Simon Akuraga, wanda aka raba wa manema labarai a safiyar Asabar.
A cewar sanarwar, marigayi Fasto Kyukyundu shi ne limamin St John da ke Geraga, kafin rasuwarsa wanda ya ba da gudunmawa mai yawa ga Kiristanci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


