Matawalle: Ministan Tsaro Ya Yi Martani kan Sace Dalibai Mata a Kebbi

Matawalle: Ministan Tsaro Ya Yi Martani kan Sace Dalibai Mata a Kebbi

  • Karamin ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle, ya fito ya yi magana kan harin da 'yan bindiga suka kai a Kebbi, inda suka yi awon gaba da wasu dalibai mata
  • Matawalle ya yi Allah wadai da harin da 'yan bindigan suka kai wanda ya jawo hallaka mataimakin shugaban makarantar da ke karamar hukumar Danko/Wasagu
  • Karamin ministan ya bayyana umarnin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba hukumomin tsaro kan sace daliban mata da 'yan bindigan suka yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Karamin ministan tsaro, Dr. Bello Mohammed Matawalle, ya yi magana kan harin da 'yan bindiga suka kai a wata makarantar kwana da ke jihar Kebbi.

Bello Matawalle ya yi tir da harin da ‘yan bindigan suka kai da daddare a makarantar sakandire ta GGCSS, Maga, cikin masarautar Zuru, karamar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta daukarwa 'yan Najeriya alkawari kan sace dalibai mata a Kebbi

Matawalle ya yi Allah wadai kan harin 'yan bindiga
Bello Matawalle yana duba sojojin kasa Hoto: Dr. Bello Matawalle
Source: Twitter

Karamin ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin hukumar tsaro a yanar gizo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun sace dalibai a Kebbi

Harin na 'yan bindigan ya yi sanadiyyar rasuwar mataimakin shugaban makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, tare da sace dalibai da dama.

Bayan sun hallaka mataimakin shugaban makarantar ne kuma suka kutsa dakin kwanan dalibai, inda suka yi awon gaba da dalibai mata masu yawa.

Miyagun yan bindigan sun je yankin ne a kan babura masu yawa, kuma suna har suka gama ta'asarsu ba wanda ya iya kai dauki don suna harbi da miyagun makamai.

Me Matawalle ya ce kan sace dalibai mata?

Matawalle ya bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a lamunta ba, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su yi aiki cikin gaggawa da haɗin kai domin ceto daliban da aka sace ba tare da bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An kashe mataimakin shugaban APC, 'yan sanda sun dauki mataki

“Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayar da umarnin cewa hukumomin tsaro na jihar su fara aiki nan take domin tabbatar da ceto daliban da aka sace cikin koshin lafiya."

- Bello Matawalle

Ya bukaci a gudanar da aikin haɗin gwiwa wajen kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika domin su fuskanci hukunci.

Matawalle ya yi Allah wadai da sace dalibai mata a Kebbi
Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle Hoto: Dr. Bello Matawalle
Source: Original

Haka kuma ya roki al’ummar yankin da su kwantar da hankula su ci gaba da harkokinsu yayin da gwamnati da jami’an tsaro ke tunkarar matsalar.

Matawalle ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayi mataimakin shugaban makarantar da dukkan iyalan da lamarin ya shafa.

“Ina rokon Allah Ya jikansa, Ya sa ya huta, Ya kuma ba iyalansa da masoyansa juriya kan wannan babban rashi."

- Bello Matawalle

Matawalle ya ga laifin Nyesom Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi tsokaci kan takaddamar da Nyesom Wike ya yi da wani jami'in sojan ruwa.

Bello Matawalle ya bayyana cewa ministan na birnin tarayya Abuja, ya yi kuskure kan cacar bakin da ya tsaya yana yi da sojan ruwan mai suna A.M Yerima.

Kara karanta wannan

Atiku ya kausasa harshe kan sace dalibai mata a Kebbi, ya gwamnatin Tinubu shawara

Karamin ministan tsaron ya ce abin da Wike ya yi bai dace da matsayin sa ba, domin bai kamata ya tsaya yana cacar baki da jami’in da ke bin umarni daga manyansa ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng