A.M Yerima: An Yi Yunkurin Kashe Sojan da Ya Takawa Wike Birki a Abuja

A.M Yerima: An Yi Yunkurin Kashe Sojan da Ya Takawa Wike Birki a Abuja

  • An ce wasu da ba a san ko su wanene ba sun bi diddigin Laftanar A.M. Yerima a Abuja, lamarin da ya haddasa fargaba da zargin yunkurin kisa
  • Rahotanni sun nuna cewa matashin jami’in sojan ruwan ya yi dabara ya kauce wa mutanen da ke cikin motocin Hilux marasa lamba a Abuja
  • Yunƙurin ya faru ne bayan rikicin sa da Ministan Abuja, Nyesom Wike, a wani filin da ake gardama a Gaduwa, hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun bayyana cewa A.M. Yerima na rundunar sojan ruwa ya tsallake wani yunkurin kisa da ake zargin an yi masa a ranar Lahadi a Abuja.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan takaddamar da ta taso tsakaninsa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kan wani filin da ake ce-ce-ku-ce a Gaduwa.

Kara karanta wannan

Rawar da Bola Tinubu ya taka a rikicin Wike da soja, A.M Yerima

Sojan Najeriya, AM Yerima
AM Yerima da aka yi zargin kai masa hari a Abuja. Hoto: Imran Muhammad|HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Vanguard ta rahoto cewa majiyoyi sun shaida cewa wasu mutanen da ke cikin motocin Hilux guda biyu marasa lamba ne suka bi jami’in a hanya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce sun yi ta bin sojan ne tun daga tashar mai ta NIPCO da ke kusa da hanyar Kubwa har zuwa hanyar Gado Nasco.

Zargin yunƙurin kashe A.M Yerima

Majiyoyin tsaro sun ce lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 6:30 na yamma, lokacin da jami’in ke kan hanyarsa.

Wata majiya ta bayyana cewa:

“Yerima ya fahimci ana bin sa, sai ya yi dabara a hanya, wanda hakan ya sa ya kuɓuta. Ana gudanar da bincike kan lamarin da muhimmanci sosai.”

Majiyoyin sun ƙara da cewa an boye wasu bayanai domin kada a gurgunta binciken da ake gudanarwa a halin yanzu.

The Guardian ta rahoto cewa masu amfani da kafafen sada zumunta a Najeriya sun bukaci gudanar da bincike kan zargin.

Rikicin Wike da A.M Yerima a Abuja

Kara karanta wannan

Sowunmi ya hango wurin da gwamnatin Tinubu ta yi kuskure a rigimar Wike da matashin soja

Zargin unƙurin kashe shi ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wani rikici da ya kunno kai tsakanin Yerima da Ministan Abuja, Nyesom Wike, a wani filin da ake gardama a Gaduwa.

A bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta, an ga Ministan na yin bahagon furuci ga jami’in, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce har sai da fadar shugaban Kasa ta dakatar da rusau a wajen.

Rikicin Wike da soja a Abuja
Yadda Wike ya yi rikici da A.M Yerima a Abuja. Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Ganau sun ce jami’an tsaro da dama ne suka yi kokarin shawo kan rikicin kafin daga bisani a samu sulhu. Jama'a da dama, fararen hula, lauyoyi da tsofaffin sojoji sun yi tir da yadda lamarin ya faru.

Matsayar ma'aikatar tsaro kan rikicin

A wani rahoton, kun ji cewa Ministan tsaro, Mohammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa babu wani jami’in soja da za a hukunta a kan aikinsa.

Tsohon gwamnan ya ce dakarun Najeriya suna aiki bisa doka, kuma gwamnati ba za ta ɗauki matakin da zai karya musu gwiwa ba.

Badaru ya yi magana ne yayin da ake cigaba da bincike kan lamarin, yayin da al’umma da hukumomi ke sa ido kan abin da zai biyo baya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng