Alaka Ta Yi Tsami Tsakanin Tinubu da Yahaya Bello? An Ji Gaskiyar Zance
- Tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya yi martani kan jita-jitar da aka yada kan alakarsa da Shugaba Bola Tinubu
- Yahaya Bello dai ya yi martanin ne bayan an yada cewa dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da shugaban kasar na Najeriya
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa har yanzu yana da cikakken goyon baya ga tazarcen Shugaba Tinubu a zaben shekarar 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kogi - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya nesanta kansa daga wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, kan alakarsa da Shugaba Bola Tinubu.
A cikin bidiyon, wata mace mai suna Joy Sadiq ta yi ikirarin cewa akwai takaddama tsakanin Yahaya Bello da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sa wa hannu da kansa, wadda ya sanya a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 16 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan
Akpabio: Shugaban majalisar dattawa ya fadi halin da yake shiga kan kashe kashe a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yahaya Bello ya nesanta kansa da Joy
Yahaya Bello ya ce ba shi da wata alaka da Joy Sadiq, banda cewa tana daga cikin wadanda lokaci zuwa lokaci kan yi ikirarin biyayya ga jam’iyyar APC ta Kogi ta hanyar da ba ta dace ba.
Ya bukaci jama’a da kafafen yada labarai su dauki maganganun Joy Sadiq a matsayin marasa tushe, kuma ba su da nasaba da shi.
Tsohon gwamnan ya ce manufar su kawai ita ce tada husuma da bata sunansa da dangantakarsa da manyan mutanen da aka ambata.
“Na lura da wasu kalamai da bidiyoyi da wata mai suna Joy Sadiq, wadda take amfani da @realmamakogi da @realmamakogi2 a Facebook da TikTok, ta yada, inda ta yi zarge-zarge marasa tushe game da dangantakata da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu."
- Yahaya Bello
Yahaya Bello ya yi watsi da zarge-zarge
Yahaya Bello ya ce ya kamata a fahimci cewa wannan matar da maganganunta ba su da alaka da shi, kuma ya yi watsi da duk wani zance da ta yi wai a madadinsa.
Ya kara da cewa zargin da Sadiq ta yi, ciki har da cewa Tinubu ya ware shi daga gwamnati ko cewa akwai batun cin amanar juna, duk karya ne, yaudara ce, kuma ba su da wata nasaba da abin da ya sani.
“Ba ta taba magana a madadina ba, ba ta taba wakiltata ba, balle gwamnatin da na jagoranta ko wani bangare na ta. Duk abin da ta fada, na kashin kanta ne kadai."
- Yahaya Bello
Alakar Yahaya Bello da Tinubu
Ya bayyana cewa dangantakarsa da Shugaba Tinubu tana da karfi, cike da girmamawa, fahimta da manufa daya ta siyasa, kuma ba abin da zai girgiza hakan.
Yahaya Bello ya kara da cewa yana da cikakken goyon baya ga sake zaben Tinubu a 2027, yana mai cewa:
“Ina goyon bayan shugaban kasa gaba daya, kuma ina kin duk wani kokari da zai karkatar da gaskiyar dangantakar mu.”

Source: Facebook
Gwamna Ododo ya umarci Kama Joy Sadiq
A gefe guda kuma, jaridar Leadership ta ce cewa gwamnan jihar Kogi, Alhaji Usman Ododo, ya bada umarnin a kama Joy Sadiq.
Wata majiya ta bayyana cewa ta na hannun jami’an tsaro, tana bayar da bayanan da ka iya taimakawa wajen gano asalin wanda ya shirya bidiyon.
Yahaya Bello ya ba 'yan majalisu umarni
A wani labarin kuma, kun ji cewa an nuna wani bidiyo wanda ya nuna tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, yana ba 'yan majalisun jihar Umarni.
A cikin bidiyon, Yahaya Bello ya bukaci mambobin majalisar dokoki na jihar da su mara wa gwamnatin Gwamna Usman Ododo baya.
A cikin jawabin da Yahaya Bello ya yi ga ‘yan majalisar, tsohon gwamnan ya umarce su da su zauna a kasa, inda ya bukaci haɗin kansu a jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

