"Yadda 'Yan CJTF Za Su Iya Kawo Karshen 'Yan Bindiga cikin Shekara 1'

"Yadda 'Yan CJTF Za Su Iya Kawo Karshen 'Yan Bindiga cikin Shekara 1'

  • Shugaban kungiyar Civilian Joint Task Force (CJTF) Farfesa Kailani Mohammed ya samo mafita kan matsalar rashin tsaro
  • Farfesa Kailani ya bayyana cewa 'yan CJTF za su iya kawo karshen ta'addanci da 'yan bindiga a cikin shekara daya
  • Shugaban na CJTF ya bayyana abin da suke bukata daga wajen gwamnati ta yi musu domin cimma hakan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban Civilian Joint Task Force (CJTF) na kasa, Farfesa Kailani Muhammad, ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro.

Farfesa Kailani ya bayyana cewa idan gwamnatin tarayya ta ba CJTF kayan aiki na zamani, za su iya kawo karshen ta’addanci da ‘yan bindiga cikin shekara daya kacal.

'Yan CJTF sun ba Shugaba Tinubu shawara
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da babban hafsan tsaro Hoto: @OfficialABAT, @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Jaridar Tribune ta kawo rahoton cewa ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Asabar, 15 ga watan Nuwamban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi bayanin ne lokacin da Mr. Charles Omini, jakadan kungiyar International Human Rights Protection Service/Forum aa yammacin Afirka, ya mika masa takardar zama abokan haɗin gwiwa a matsayin shugaban West African Joint Task Force.

Kara karanta wannan

Rigima da soja: Kungiya ta bukaci Tinubu ya kori Wike, ta fadi wanda ya kamata ya maye gurbinsa

Me 'yan CJTF suke bukata?

Farfesa Muhammad ya bukaci gwamnati ta ba CJTF goyon bayan da ya dace, yana mai cewa:

"Idan aka ba mu goyon baya yadda ya kamata, za mu murkushe su.”

Ya ce CJTF ta san yankunan da ‘yan bindiga ke buya a jihohin da matsalar rashin tsaro ke faruwa.

“Idan har muna nufin magance matsalar, mun san inda suke, mun san wuraren da suke boye.”

- Farfesa Kailani Muhammad

An Shugaba Tinubu shawara

Shugaban na CJTF ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sanya dukkan hafsoshin su yi alkawari alkawari tare da hadin gwiwar CJTF, domin a kawar da rashin tsaro cikin shekara daya, rahoton PM News ya tabbatar da labarin.

“Muna kira ga shugaban kasa ya ba hafsoshin tsaro wa’adi na shekara ɗaya. Su rattaba hannu cewa cikin shekara guda, tare da hadin gwiwa da mu, za su kawar da rashin tsaro a Najeriya."

Kara karanta wannan

An fadi gaskiya kan ikirarin sace Birgediya Janar yayin gwabzawar sojoji da ISWAP

"Idan ba su yi ba, su yi murabus, a samo wani rukuni ya yi aikin. Bai kamata a kyalesu a haka nan ba, ya kamata a zaburar da su a nuna musu da gaske ake yi."

- Farfesa Kailani Muhammad

Farfesa Kailani Muhammad ya bukaci gwamnati ta ba CJTF kayan aiki masu kyau da fasahar zamani don su iya tunkarar kalubalen tsaro yadda ya kamata.

'Yan CJTF sun mika kokon bararsu ga Shugaba Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Me ya tabarbarar da rashin tsaro?

Ya ce matsalar tsaro na kara samun karfi saboda iyakar kasar nan ta bude sosai, yana mai cewa sun gano fiye da hanyoyi 2,000 da ake shiga da fita daga Najeriya.

“Mu mun riga mun gano dukkan hanyoyin. Idan gwamnati ta taimake mu, muna bukatar CCTV kamar yadda ake yi a Mexico da Amurka."
"A saka su a tazarar kilomita 100 domin a hango duk wani motsi na ‘yan ta’adda, ta hanyar bayanan leken asiri. Akwai AI yanzu.”

- Farfesa Kailani Muhammad

Ya jaddada cewa goyon bayan gwamnati zai ba su damar taka rawar gani wajen kare kasa da magance barazanar tsaro.

'Yan bindiga sun kashe dan siyasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun hallaja tsohon dan takarar kujerar majalisar wakilai a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Saraki ya samo mafita ga babbar jam'iyyar adawa

Hon Umar S. Fada Moriki ya rasa ransa ne a kan hanyar Tsafe da ke jihar a yankin Arewacin Najeriya.

Marigayin ya rasa ransa ne bayan wasu ’yan bindiga sun kai masa hari a kan hanyar Tsafe, inda suka kashe shi har lahira.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng