Akpabio: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Fadi Halin da Yake Shiga kan Kashe Kashe a Najeriya
- Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya koka kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
- Godswill Akpabio ya bayyana cewa yana shiga cikin mawuyacin hali idan ya ji rahoton cewa an kashe mutane
- Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na bakin kokarinta wajen magance matsalar rashin tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi magana kan kashe-kashen da ake fama da su a jihar Plateau.
Godswill Akpabio ya ce dawo da zaman lafiya da hadin kai a jihar Plateau da kasa baki daya alhakin gwamnatin Najeriya ne, ba wai na kasashen waje ba.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Akpabio ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar a Jos Polo Field, yayin bikin tarbar masu sauya sheka zuwa APC a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio ya ce gwamnati na kokari
Ya jaddada cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuduri aniyar kawo karshen rikice-rikice da tarzoma a Plateau da duk fadin kasar.
“Muna rokon Allah Mai Girma Ya taimaka mana mu dawo da zaman lafiya a Plateau. Duk wanda zai mulki Plateau dole ya kasance mai kaunar zaman lafiya. Wannan ita ce jam’iyyar da ke kula da ku."
"Na zo nan a madadin shugaban kasa domin tabbatar muku cewa za mu yi duk mai yiwuwa don tabbatar da zaman lafiya."
"Ba wasu mutane daga waje ne za a kawo muku zaman lafiya ba, mu ne dole mu tabbatar da zaman lafiya, mu zauna lafiya da juna. Dolenne Najeriya ta samu zaman lafiya kafin ci gaba ya samu.”
- Godswill Akpabio
Akpabio ya tabbatar wa mutanen Plateau cewa gwamnati ba za ta yi shiru ba, domin za a magance damuwarsu.
Wane hali Akpabio yake shiga kan kashe-kashe?
“Ina kuka duk lokacin da na ji an kashe mutum, ko yaro ko babba. Wannan matsalar ba yau ta fara ba; tun shekaru da dama ne mutane ke mutuwa a Plateau."
"Najeriya na kuka. An zubar da jini da yawa, kuma hakan na damun mu. Shugaban kasa ma ba ya farin ciki.”
- Godswill Akpabio
Shugaban majalisar dattawan ya ce matsalar tun 2010 ta samo asali, yana mai cewa rahotannin da ake amfani da su a duniya sun fito ne tun wancan lokaci.

Source: Facebook
Ya ce yawaitar kashe-kashen, korar jama’a da lalata dukiyoyi ba abin da za a musanta ba ne, kuma gwamnati za ta kara kaimi wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Plateau da fadin Najeriya.
Akpabio ya yi kira ga mutanen Plateau da su goyi bayan Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan zai kawo gagarumin cigaba ga jihar.
An yi yunkurin tsige Akpabio
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu sanatoci a majalisar dattawa sun yi yunkurin tsige Godswill Akpabio daga mukaminsa.
Tsohon gwamnan jihar Abia kuma sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya tabbatar da labarin yunƙurin tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Sanata Kalu ya ce duk da kokarin da aka yi na tsige Akpabio, amma hadin kansu ya taimaka shugaban majalisar ya tsira da kujerarsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


