Sulhu da 'Yan Bindiga: Sheikh Gumi Ya Ragargaji Masu Sukarsa, Ya Fadi Nasarorin da Ya Samu
- Wasu mutane sun dade suna kiraye-kirayen da a cafke Sheikh Ahmad Abubakar Gumi kan rawar da yake takawa wajen sulhu da 'yan bindiga
- Sanannen malamin addinin Musuluncin ya fito ya ragargaji mutanen da ke kiran hukumomi su kama shi
- Sheikh Gumi ya bayyana cewa abubuwan da yake yi, yana yin su ne domin ganin an samu zaman lafiya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi martani kan masu neman a kama shi saboda shiga sulhun da yake yi da 'yan bindiga.
Sheikh Gumi ya yi tur da irin kiran da wasu ke yi na a kama shi saboda tsokacin da yake yi kan batun ‘yan bindiga da tsaron kasa.

Source: Facebook
A cikin wani rubutu da ya wallafa a Facebook a ranar Lahadi, malamin ya fito ya kare kansa.

Kara karanta wannan
'Sai mun biya': Al'umma sun fadi makudan kudi da suke ba 'yan bindiga domin kariya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Gumi na shan suka
Sheikh Gumi, wanda tsawon shekaru yake taka rawa a matsayin mai shiga tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga, ya sha samun yabo daga wasu da suka yi amince da hanyarsa, da kuma suka daga masu adawa da shi.
Wasu daga cikin masu suka suna tuhumarsa da kare ‘yan ta’adda, suna zargin cewa ya fi goyon bayan tattaunawa da su maimakon amfani da karfi.
Sheikh Gumi ya kira masu sukar nasa da mutane marasa mutunci, marasa tarbiyya, marasa kishin kasa, yana mai cewa sun fi son hayaniya da tada kura fiye da fuskantar gaskiya kan matsalar tsaro.
Sheikh Gumi ya soki masu sukarsa
Gumi ya yi Allah-wadai da kiraye-kirayen da ake yi na a kama shi, yana mai cewa bai aikata laifi ba, domin tattaunawa da ‘yan bindiga da nufin samar da zaman lafiya ba laifi ba ne.
Ya kara da cewa masu kira da a kama shi, son zuciya, jahilci da rashin jure ra’ayoyin wasu ne ke damunsu.
“A Kama shi!!! Waɗannan su ne kalmomin da marasa mutunci, marasa kishin kasa za su iya furtawa."
- Sheikh Ahmed Abubakar Gumi
Sheikh Gumi ya yi zargin cewa masu neman a kama shi sun mayar da kokarinsa na zaman lafiya batun siyasa maimakon nazarin tabarbarewar tsaron kasar.
Sheikh Gumi ya jagoranci sulhu da 'yan bindiga
Sheikh Gumi ya tunatar da yadda ya jagoranci wani babban shiri na tattaunawa a dajin Sabon Garin Yadi, karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, a watan Janairun 2021.
Ya ce a wannan tafiyar, kwamishinan ’yan sanda na Kaduna a lokacin, wanda ya wakilci IGP, ya yi masa rakiya.
A cewarsa, taron ya samu halartar fiye da ‘yan bindiga 600 da shugabanninsu, domin shirin shigar da su cikin zaman lafiya da mika makamansu.
“Mun yi wa sama da ‘yan bindiga 600 wa’azi tare da shugabanninsu, kuma sun amince su ajiye makamai a kan gwamnati ta ba su tsaro da muhimman abubuwan more rayuwa."
- Sheikh Ahmed Abubakar Gumi

Source: Facebook
Sheikh Gumi ya ce tattaunawar ta kasance karara, bisa doka, kuma da sanin hukumomi. Ya ce dukkan sharuddan da ‘yan bindigar suka gabatar, kamar samar da abubuwan more rayuwa da kariya daga kama su ba tare da dalili ba, ba a cika musu ba, wanda hakan ya sa tattaunawar ta rushe.
Gumi ya nuna takaici cewa maimakon mutane su tambayi dalilin da yasa gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyar, sai suka mayar da hankali wajen kai hari a kansa.
“Manufar wannan taro ita ce rage tashin hankali domin ‘yan bindiga su mika makamai su rungumi zaman lafiya."
"Fiye da 600 sun amince su ajiye makamansu, amma sharuddan da suka gabatar ba a aiwatar da su ba."
- Sheikh Ahmad Abubakar Gumi
Sheikh Gumi ya dage cewa duk abin da ya yi na cikin kishin kasa ne, don haka ya ga babu wani dalili da zai haifar da kiraye-kirayen kama shi.
Sheikh Gumi ya musanta tserewa zuwa Turkiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Ahmed Abubakar Mahmud Gumi, ya yi magana kan zargin ya tsere zuwa kasar Turkiyya.
Malamin addinin Musuluncin ya musanta cewa ya gudu zuwa Turkiyya saboda tsoron barazanar shugaban kasar Amurka, Donald Trump.
Sheikh Gumi ya bayyana cewa ko kadan ba tserewa ya yi ba, domin tun kafin Trump ya yi barazanarsa ya samu bizarsa zuwa Turkiyya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

