Musulmai Sun Maka Gwamna Guda a Kotu kan Mika Makarantar Gwamnati ga Coci

Musulmai Sun Maka Gwamna Guda a Kotu kan Mika Makarantar Gwamnati ga Coci

  • Gwamna Monday OKkpebholo zai kare kansa bayan kungiyar Musulmi ta maka shi da gwamnatinsa game da makarantar gwamnati
  • Musulmai a jihar Edo sun kai gwamnati kotu kan mika makarantun gwamnati ga cocin Katolika ba tare da tuntubar sauran bangarori ba
  • Masu kara sun ce matakin ya sabawa sashe 38 da 42 na kundin tsarin mulki, suna neman kotu ta hana sake mika makarantun

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benin-Ciyu, Edo - Musulmai a jihar Edo sun shigar da kara a kotu kan Gwamnatin Jihar Edo da Gwamna Monday Okpebholo.

Kungiyar ta dauki matakin ne saboda mika wasu makarantun firamare da sakandare na gwamnati ga cocin Katolika.

An maka gwamna a kotu bayan mika makaranata ga coci
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo. Hoto: Sen. Monday Okpebholo.
Source: Twitter

Musulmai sun maka gwamnan Edo a kotu

Kungiyar Edo Muslims for Good Governance (EMGG) ce ta shigar da karar a madadin kungiyar dalibai Musulmi (MSSN) reshen Edo-Delta, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

'Sai mun biya': Al'umma sun fadi makudan kudi da suke ba 'yan bindiga domin kariya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sirajudeen Muhammad da Abdullahi Umar, wadanda suka shigar da karar, sun ce wannan mataki ya sabawa sashe na 38 da 42 na kundin tsarin mulki.

Sun ce an yi hakan ne ba tare da tuntuba da la’akari da sauran al’ummomi ba, sun nemi kotu ta dakatar da mika sauran makarantun har sai an bi ka’ida yadda ya dace.

Masu karar sun bukaci kotu ta tantance ko mika makarantun gwamnati kai tsaye ga cocin ya dace da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Musulmai sun kalubalanci gwamna kan makarantu

Haka kuma suna cewa rashin tuntubar Musulmai da sauran bangarori ya saba wa gaskiya, adalci da tsarin halascin gwamnati da kundin tsarin mulki ya tanada.

Suna kuma kalubalantar sahihancin mika makarantun da aka riga aka mika, ciki har da makarantar mata St. Maria Goretti a Benin, Kwalejin Annunciation a Irrua.

Sauran sun hada da makarantar mata ta St. Angela’s a Uzairue, da makarantar firamare ta Obaseki a Benin, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Tinubu: Fasto ya tura sako ga Trump kan kashe kashe da ake a Najeriya

Sun ce wannan mataki ba shi da hurumin doka, don haka ya zama marar inganci wanda ya ke cike da rashin adalci.

Musulmai sun maka gwamnan Edo a kotu
Taswirar jihar Edo da APC ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

Rokon kungiyar Musulmi ga kotu

Haka kuma sun ce jerin wasu makarantun 36 da aka shirya mika wa cocin Katolika ya nuna wariya, don haka bai dace da kundin tsarin mulki ba.

Sun nemi kotu ta bayyana cewa malamai masu addinai daban-daban da ke aiki a makarantun ba za a tilasta musu canji ko a kore su ba bisa sababbin tsare-tsaren Cocin Katolika.

Sun kuma nemi kotu ta umurci gwamnati ta cigaba da kula, jagoranci da gudanar da makarantun gwamnati kamar yadda dokokin ilimi da kundin tsarin mulki suka tanada.

Alkalin kotun, Ovenseri Aghamieghen Otameri, ya dage shari’ar zuwa 9 ga Disamba, 2025, bayan an sanar da shi cewa gwamnati ba ta gabatar da martani kan karar ba.

Gwamna ya roki Musulmi kan zaben Tinubu

A wani labarin, Gwamna Monday Okpebholo ya yi kira ga al’ummar Musulmi su ci gaba da marawa Shugaba Bola Tinubu baya.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Dalilin da ya sa Amurka ba za ta saka wa Najeriya takunkumi ba

Okpebholo ya ce goyon bayansu na da matuƙar muhimmanci ga nasarar sauye-sauyen da gwamnati ke yi.

Gwamnan ya sake nanata alkawarin kawo Tinubu kan gaba a zaben 2027, ciki har da niyyarsa ta samar da kuri’u miliyan 2.5 daga Edo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.