An Tafka Babban Rashi, Malamin Addini Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Taraba

An Tafka Babban Rashi, Malamin Addini Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Taraba

  • Cocin Katolika na Wukari a jihar Taraba ya tabbatar da rasuwar babban malamin addinin Kirista bayan rashin lafiya
  • Marigayin ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya Wukari, inda ya shafe shekaru yana hidimar Allah cikin tawali’u da jajircewa
  • Ana shirin gudanar da jana’izarsa a St Mary da ke Wukari, tare da yi masa wake ranar 19 ga Nuwamba da kuma jana’iza ranar 20 ga wata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Wukari, Taraba - Cocin Katolika ta Wukari a Jihar Taraba ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin manyan limamanta da ya ba da gudunmawa.

An tabbatar da rasuwar Fasto Nicholas Kyukyundu, wanda ya riga mu gidan gaskiya bayan doguwar rashin lafiya.

Babban Fasto ya bar duniya a Taraba
Marigayi Fasto Fasto Nicholas Kyukyundu kafin rasuwarsa. Hoto: Jolly Nanen Sylvester.
Source: Facebook

An yi rashin babban Fasto a jihar Taraba

Sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban cocin, Rabaran Simon Akuraga, wanda aka raba wa manema labarai a safiyar Asabar 15 ga watan Nuwambar 2025, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Abin takaici: Yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar majalisar tarayya a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, marigayi Fasto Kyukyundu shi ne limamin St John da ke Geraga, kafin rasuwarsa wanda ya ba da gudunmawa mai yawa ga Kiristanci.

Marigayin ya rasu ne da rana a ranar Litinin, 11 ga Nuwamba 2025, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Wukari, yana da shekara 66 da haihuwa.

An haifi Faston a ranar 6 ga Janairu 1959, kuma aka ba shi mukami a matsayin limamin Katolika ranar 29 ga Yunin shekarar 1991.

Al'ummar Kiristoci sun shiga jimami bayan mutuwar Fasto
Taswirar jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas. Hoto: Legit.
Source: Original

Yaushe za a fara shirye-shiryen birne shi?

Sanarwar ta bayyana cocon ya samu labarin rasuwarsa “da bakin ciki amma da yarda da nufin Allah, inda ya ce an shirya wa marigayin jana’iza a St Mary’s Cathedral, Wukari.

Za a gudanar da wake ranar Laraba, 19 Nuwamba 2025, da ƙarfe 5 na yamma, sannan jana’iza ranar Alhamis, 20 Nuwamba 2025, da ƙarfe 10 na safe.

Cocin ya bayyana marigayin a matsayin bawan Allah nagari wanda ya yi hidima cikin tawali’u da jajircewa tun daga lokacin da aka naɗa shi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da sake nada Buba Marwa shugaban NDLEA zuwa 2031

Sun ce ya koyar da mutane halaye na tausayi, imani, da kulawar addini, kuma ba za a taɓa mantawa da shi cikin al’umma ba.

Mabiya cocin Katolika daga sassa daban-daban na Taraba sun fara tura sakonnin ta’aziyya ga cocin, inda da dama suka kira shi garkuwa ga mabiyansa.

Har ila yau, an bayyana marigayin a matsayin mutum mai “son zaman lafiya” saboda irin ƙoƙarin da ya yi a rayuwarsa.

Fasto Fagun ya yi bankwana da duniya

Mun ba ku labarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike da sakon ta’aziyya ga cocin Katolika da al’ummar Kirista bisa rasuwar babban malami.

An tabbatar da rasuwar Fasto Michael Olatunji Fagun, tsohon malamin coci da ya ba da gudunmawa sosai da ya ke raye.

Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin bawan Allah mai tsantseni wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa bishara da kuma tabbatar da cewa mabiya sun zauna lafiya da sauran addinai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.